Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TSARO: Buhari Ya Bukaci Sojoji Su Gaggauta Murkushe ’Yan Bindigar Da Suka Addabi Jihar Neja


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba rundunar sojin kasar umarni su yi amfani da karfi wajen kawo karshen ‘yan bindigar da ke kashe-kashen al’ummar da basu ji ba basu gani ba, da kuma masu garkuwa da mutane a Jihar Neja.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Lahadi, inda yace shugaban ya bayar da umarnin ne ga hedikwatar rundunar tsaron kasar don fara aikin cikin gaggawa.

A cikin sanarwar, shugaba Buhari ya ce a matsayinsa na babban kwamandan sojojin Najeriya a shirye ya ke ya daura damarar gagarumin farmakin soji a jihar Neja.

Jihar Neja dai na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindigar da kotu ta ayyana a matsayin ‘yan ta’adda a baya-bayan nan da kuma mayakan Boko Haram da ke tserewa daga jihohin arewa maso yamma da sojoji ke luguden wuta a kan su da kuma a arewa maso gabashin kasar nan kamar su jihohin Borno.

Shugaban ya kuma mika sakon ta’aziyya da alhini ga al’ummar jihar Naje sakamakon hare-haren yan ta’addan na baya-bayan nan inda ya jadada cewa sojoji zasu murkushe miyagun irin.

Haka kuma, shugaba Buhari ya jadada cewa, samar da tsaro nauyi ne da rataya a wuyan gwamnati da alumma kuma baiwa hukumomin tsaro hadin kan da ya kamata wata hanya ce da zata iya kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar baki daya.

A cewar shugaban, a shirye gwamnatinsa take ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukan jihohin kasar inda ya yi imanin cewa, idan har yan Najeriya sun ba gwamnati cikakken hadin kai tabbas kasar zata sami nasarar shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Idan ana iya tunawa, ‘yan bindigar da ke tserewa a dazukan jihar Zamfara sun far wa wasu kauyukan cihar Zamfara inda rahotanni suka ce sun halaka mutane sama da 150 baya ga kisan akalla wasu mutane 13 da suka yi makon jiya a sakamakon wani hari da ’yan bindigar suka kai da tsakar rana a kauyukan Nakundan da Wurukuci da ke karamar hukumar Shiroro na Jihar Neja.

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa, wasu ‘yan bindiga da ba’a iya tantance adadinsu ba a kan babura sun far wa al’umman garin Damari a karamar hukumar Binin Gwari inda al’umma suka yi ta tserewa don gujewa rasa ransu.

Harin na jihar Neja dai na zuwa ne cikin kasa da makonni biyu da ’yan bindiga suka kai wa wata ma’aikata a madatsar ruwa ta garin Zungeru, inda suka halaka mutane biyu baya ga yin awon gaba da wasu ’yan kasar China uku a lokacin kai harin.

XS
SM
MD
LG