Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korona Bairos: Femi Adesina Ya Jadada Cewa Shugaba Buhari Na Nan Cikin Koshin Lafiya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/Femi Adesina)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/Femi Adesina)

"Idan gwaji ya tabbatar da cewa wani na kusa da shugaba Buhari ya kamu da cutar Korona ana bukatar mutumin ya kebance kan sa har sai ya warke kuma ya sake gwajin da ya tabbatar da hakan"

Mai ba shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya sake jadada cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na cikin koshin lafiya duk da cewa wasu mukarrabansa sun kamu da cutar korona bairos.

Adesina ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels.

Adesina ya kara da cewa masu taimaka wa shugaban kasa da suka kebance kansu bayan gwajin da ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar COVID-19, ya tabbatar da cewa su ma kamar sauran al’umma, mutane ne masu jini a jiki, kuma ba su da kariya ta daban da saura mutane ga abubuwan da ke faruwa a kusa da su walau na lafiya ko wani abu na daban.

Kazalika, Femi Adeshina ya ce ya yi imani da ubangijinsa ko da ya kamu da cutar korona sakamakon mu’amalla da abokan aikinsa zai warke kamar yadda wadanda suka kamu a baya suka warke.

A game da maganar adadin mataimakan shugaba Buhari da suka kamu da cutar ta korona a baya-bayan nan, Adesina ya ce wannan ba huruminsa ba ne saboda ba shi ne likitan fadar shugaban kasa ba.

"Idan gwaji ya tabbatar da cewa wani na kusa da shugaba Buhari ya kamu da cutar Korona ana bukatar mutumin ya kebance kan sa har sai ya warke kuma ya sake gwajin da ya tabbatar da hakan" in ji Adesina.

A karshen makon Ajiya ne jaridar Premium Times ta bayyana sunayen wadanda suka kamu da cutar korona a cikin mukarraban shugaba Buhari ciki har da dogarin shugaban wato ADC, Yusuf Dodo, babban jami’in tsaronsa wato CSO, Aliyu Musa, da mai magana da yawun shugaban, Mal. Garba Shehu.

A ranar Talatar makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19 na Pfizer Biontech karo na uku da aka yiwa taken 'karfafa kariya' yayin da Najeriya ta shiga zango na hudu a bullar cutar coronavirus.

Haka kuma, a ranar talatar makon jiya ma sai da mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, ta umarci dukkan ma’aikatanta da su tafi hutu har sai wani lokaci da za ta sanar da dawowan su aiki.

Idan ana iya tunawa, a shekarar da ta gabata, Aisha Buhari ta ba da irin wannan umarnin a sakamakon barkewar annobar korona birus.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG