Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Fashin Daji ‘Yan Ta’adda Ne - Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Al’umomin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama ga ‘yan fashin daji wadanda kan yi garkuwa da mutane su nemi kudin fansa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya ‘yan ta’adda ne.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Channels a fadarsa da ke Abuja.

An dade ana kai ruwa rana akan gwamnatin ta Buhari ta ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda saboda irin ta’asar da suke aikatawa.

Al’umomin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama ga ‘yan fashin daji wadanda kan yi garkuwa da mutane su nemi kudin fansa.

“Mun ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, za kuma mu tafiyar da su a matsayin hakan.” Buhari ya ce yayin hirarsa da Channels.

Shugaban na Najeriya ya kuma ce ana samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan fashin dajin yana mai jaddada cewa za su yi maganinsu.

Majalisar dokokin kasar ta taba neman gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda.

A bara wata kotun tarayya ta ayyana ‘yan fashin dajin a matsayin ‘yan ta’adda bayan wani koke da gwamnatin tarayya ta gabatar a gaban kotun kan a ba ta iznin ta yi hakan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG