Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yi wani taro na musamman da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma domin duba yadda za a warware matsalolin tsaro a jihar.
Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta sha fama da matsalar hare-haren ‘yan aware, wadanda sukan musanta hannu a rikicin.
Rahotanni da dama sun nuna yadda ake yawan kashe jami’an tsaro a jihar ta Imo.
Ko a karshen makon da ya gabata, wasu ‘yan bindiga da hukumomin tsaro suka ce ‘yan aware ne, sun kai hari gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Farfesa George Obiozor.
Gabanin hakan kuma, wasu ‘yan bindigar sun far wani caji ofis din ‘yan sanda inda suka halaka wasu daga cikinsu.
Wakilin Muryar Amurka a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Umar Faruk Musa ya ruwaito cewa, baya ga gwamnan na Imo, Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma gana da ministan kula da makamashin wutar lantarki Abubakar Aliyu.
Sassan daban-daban na kasar ta Najeriya sun jima suna fama da karancin wutar ta lantarki, lamarin da ya durkusar da harkokin kasuwanci da dama.
Ku Duba Wannan Ma Shugaba Buhari Ya Yi Sammacin Gwamnan Jihar Imo Game Da Halin Tsaro a Jihar.A makon da ya gabata hukumomi suka shawo kan wata matsala ta katsewar wutar lantarki a jihohi bakwai har da Birnin Abuja.
“Shugaba Muhammadu Buhari, yau (Litinin) ya komo aiki a ofis, saboda haka, damuwa da yake ciki da wadannan abubuwan, shi ya sa ya dauki wannan mataki na farko, don ya sadu da shugabannin na wadannan sassa daban-daban, don ya ji ina aka kwana, kuma wane mataki ake dauka.” In ji Kakakin Buhari, Malam Garba Shehu.
Kazalika Buhari ya gana da Farfesa Doyin Salami da ke ba shi shawara kan tattalin arzikin domin tsara mafita akan lalurorin tattalin arzikin da suka dabaibaye kasar.
Gabanin ya koma Najeriya daga ziyarar da ya kai Birtaniya, Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan halin da kasar ta shiga, yana mai cewa gwamnatinsa na daukan matakan da za su shawo kan matsalalolin.
‘Yan Najeriya da dama sun yi ta korafi kan yadda ake samun karin tabarbarewar al’amaru a kasar, wadanda suka hada da karancin man fetur, wutar lantarki, rashin tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Saurari cikakkiyar hirar Umar Faruk Musa da Malam Garba Shehu daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5