Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Za Su Dinga Takawa Daga Legas Zuwa Ibadan Idan Ba Mu Dauki Mataki Ba - Buhari


SHUGABA MUHAMMADU BUHARI
SHUGABA MUHAMMADU BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bada fifiko kan ayyukan samar da ababen more rayuwa shi ne zai rage wahalar da ake fama da su a wasu sassan Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce, daukar matakan gaggawa su na taimakawa, musamman yadda aka yi gaggawar kammala aikin tituna da layin dogo na shiga hanyar Legas zuwa Ibadan wanda ya inganta zirga-zirga sosai.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar yau Talata, Buhari ya ce “Buri na a bayyane ya ke, duk da raguwar albarkatun da ake samu, ina so in yi maganin ababen more rayuwa a fadin kasar nan,” in ji shugaban kasar yayin da ya gana da tawagar jihar Kaduna, karkashin jagorancin Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, da mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balaraba.

“Babu wata kasa da za ta ci gaba ba tare da ababen more rayuwa ba. A da akwai layin dogo, mutanen Kaduna musamman mutanen Kudancin Kaduna za su tuna da haka."

"Wace kasa ce za ta iya samun ci gaba ba tare da hanyoyi, jirgin kasa da wutar lantarki ba? Shi ya sa na so in daidaita abubuwan more rayuwa, sanin cewa 'yan Najeriya na da son gasa, kuma za su fuskanci kasuwancinsu idan akwai hanyoyi, jirgin kasa da wutar lantarki," in ji shi.

Shugaban ya ce an rage kalubalen zirga-zirga da yankin Kudu maso Yamma ke fuskanta.

“Mutanen Kudu maso Yamma za su ga banbancin a tsakanin Legas da Ibadan a yanzu, da a ce ba mu yi abin da muka yi ba a yanzu, da mutane suna takawa domin babu hanyoyi, da layin dogo, kuma akwai rashin tsaro sosai.

“Amma muna godiya ga kasashen duniya. Muna godiya ga masu zuba jari na kasar China, wadanda suka zo suka tallafawa ayyukan sufuri na Legas zuwa Ibadan, '' in ji shi.

Shugaban ya yabawa gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai kan sauyin da jihar ta samu, tare da bunkasar ababen more rayuwa da harkokin tattalin arziki.

“Ina mika godiyata ga gwamnan da ya yi haka. Na dade ina zaune a Kaduna kafin na zo nan, amma yanzu zan bukaci na'urar zamani don zagayawa saboda sauyin da aka samu a jihar,” inji shi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG