Shugaban kasar zai gana a lokuta daban-daban da su inda zai nemi karin haske kan al’amuran jihar Imo da bangaren wutar lantarki da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Idan ba a manta ba, shugaban kasar a lokacin da yake yin Allah wadai da tashe-tashen hankula a jihar ta Imo biyo bayan lalata gine-ginen ofishin ‘yan sanda da gidan Farfesa George Obiozor, da kuma shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, ya yi alkawarin sake duba harkokin tsaro da halin da ake ciki a kudu maso gabashin Najeriya.
Shugaba Buhari ya kuma bayyana damuwarsa kan matsalar wutar lantarki da ake yawan samu, inda ya nemi gafarar ‘yan Najeriya tare da bada tabbacin samun sauki cikin gaggawa.