Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Kadu Da Rasuwar Magajin Garin Sokoto – Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya)
Shugaba Buhari (Facebook/Gwamnatin Najeriya)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ya kadu matuka da rasuwar Magajin Garin Sokoto.

A ranar Asabar Magajin Garin na Sokoto, Hassan Danbaba Marafa ya rasu. Marigayin jika ne ga Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello.

“Na kadu, ta yadda ba zan iya cewa komai ba. Magajin Garin Sokoto ya bar wani gibi da zai yi wuyan cikewa a Masarautar da kasa baki daya.”

Cikin wata sanawar da Buhari ya fitar ta hannun Kakakinsa Malam Garba Shehu, shugaban na Najeriya ya kwatanta marigayin a matsayin “mutum mai yawan fara’a.”

“Ba za a manta da shi ba, saboda rawar da ya taka wajen zama jakada wajen adana al’adun gargajiyar masarautar ta Sokoto.” Sanarwar ta ce.

“Ina mai addu’a da mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da ya bari, da gwamnatin jihar Sokoto. Allah ya sa ya huta.” Buhari ya ce.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG