Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Tafi Ethiopia Taron Kungiyar AU


Shugaba Buhari, yayin ziyarar da ya kai jihar Borno (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari, yayin ziyarar da ya kai jihar Borno (Facebook/Bashir Ahmad)

Kwana hudu ake sa ran Buhari zai yi a kasar ta Ethiopia yayin wannan ziyara a cewar wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kama hanyar zuwa kasar Ethiopia a yau Alhamis don halartar taron kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU.

Taron zai gudana ne a Addis Ababa, babban birnin ta Habasha a karo na 35.

Kwana hudu ake sa ran Buhari zai yi a kasar ta Ethiopia yayin wannan ziyara a cewar wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin kasashen nahiyar inda za su tattauna kan batutuwan da suka shafi neman mashala ga matsalolin da suka danganci siyasa, tattalin arziki da sauran larorin da ke addabar nahiyar.

Sanarwar ta kara da cewa Buhari zai kuma halarci tarukan kulla hulda da wasu shugabanni a gefen taron, musamman kan yadda za a yaukaka harkokin cinikayya, tsaro da samar da ci gaba mai dorewa.

A watan Oktobar bara, Buhari ya kai ziyara kasar ta Ethiopia inda ya halarci bikin rantsar da Firai Minista Abey Ahmed a wa’adi na biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG