Borno: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kaddamar Da Shirin “Sauya Hali”

Kwamishinan Jahar Borno Damian Chukwu Yana Kaddamar Da Shirin Sauya Hali

Runudar ‘yan sandan jahar Borno ta kaddamar da shirin ‘Canji Zai Fara Daga Kaina’ a wani yunkurin hana jami’an tsaro karbar na goro a hannun jama’a ko tursasawa mutane wani abin da ya saba doka.

A lokacin da Kwamishinan ‘yan sandan jahar Borno Damian Chukwu, ke kaddamar da shirin ‘Canji zai fara daga kaina’ yace zasu hukunta duk wani jami’in tsaro da aka samu yana karbar kudi wajen belin duk wani wanda ake tuhuma.

Jahar Borno ta zamanto jahar farko da ta kaddamar da wannan shiri. An dai kaddamar da shirin ne a tsakiyar birnin Maiduguri, wanda ya samu halartar kusan dukkannin jami’an dake aiki a jahar da ‘yan jaridu da sauran dukkannin masu aikin wayar da kan al’umma.

Damian Chukwu, yace zasu hukunta duk wani jami’in ‘dan sanda da suka kama yana karya doka wajen gudanar da aikinsa, wanda ya hada da karbar cin hanci ko na goro a gurin jama’a. Inda ya kara da cewa beli kyauta ne a ko ina, kuma bayan kaddamar da wannan shiri zasu kafe wasu bayanan da zasu nuna beli kyauta ne.

Kwamishinan yace ya bayar da lambobin wayarsa ga jama’a domin a shaida masa duk lokacin da wani jami’in ‘yan sanda ya nemi a bashi kudi wajen beli. Rundunar ‘yan sandan zata dauki matakin rage mukami zuwa kora daga aiki duk lokacin da wani jami’i ya karya dokar.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Borno: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kaddamar Da Shirin “Sauya Hali” - 3'42"