Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaddamar Da Shirin N Power A Jahar Adamawa


Masu Cin Gajiyar Shirin N-Power Na Jahar Adamawa
Masu Cin Gajiyar Shirin N-Power Na Jahar Adamawa

Matasa 3,811 ne suka anfana daga shirin gwamnatin tarayya mai lakabi da N-Power Progromme rukunin farko a jihar Adamawa.

Da yake kaddamar da shirin, gwamnan jahar Sanata Mohammadu Umaru Jibirilla Bindow, ya nuna takaicin sa da yadda aka yi rabon guraben aikin sakanin kananan hukumomi, inda wasu ke da hudu, wasu kuma ke da fiye da 700 wanda ya danganta da rashin kyakkyawar fadakarwa ga su matasa.

Sai dai madugun shirin a jahar Kwamanda Usman Sali Bodes, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, cewa rikicin Boko Haram wanda ya tarwasa mutane zuwa sassa daban-daban da kuma anfani da yanar gizo na daga cikin dalilan da suka sa aka sami irin wannan sakamakon a wasu kananan hukumomi.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin Rita Fidelis Chagwa, wadda ta yi jawabi a madadin sauran matasan ta bayyana tsarin da cewa ba karamin taimako zaiyi ga wadanda suka kammala karatunsu wajen rage zaman kashe wando da fadawa cikin miyagun ayyuka.

Domin karin bayani ga rahotan Sunusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG