Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO ta fada jiya Laraba a cikin rahotonta tana cewa akalla kashi 35 cikin dari na asibitoci 743 a jihar sun lalace kwatakwata.
Jami’ai suka ce wannan adadi ya bayyana ne a rahoton farko bayan da hukumar kiwon lafiya ta duniya da hukumar kiwon lafiya ta jihar Borno suka yi wani tsarin tattara labarai a kan matsayin aikin kiwon lafiya a jihar.
Wakilin huklumar kiwon lafiya ta duniya a Najeriya Wondi Alemu yace babban aiki da hukumar ta sa a gaba shine ceto rayuka da kare yaduwar cuta tsakanin mutane miliyon shida dake da bukatar jinya cikin gaggawa.
Rahoton yace an kafa kimanin asibitoci na wucin gadi guda dari a jihar Borno don amsa bukatun jama’a na kiwon lafiya ciki har da kananan asibitoci 49 masu kulawan gaggawa a sansanonin ‘yan gudun hijira.