Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kubutar Da Mutane 605 Daga Dajin Sambisa


Rundunar sojan Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri, tace ta samu nasarar kubuto da wasu mutane 605 a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram dake fake a dajin Sambisa.

An samu nasarar kubuto da wadannan mutane ne sakamakon ci gaba da kai hare hare da rundunar sojan Najeriya ta ke yi a dajin Sambisa. Kwamandan rundunar sojan shiyya ta bakwai majo janar Leo Irabor, ya shaidawa manema labarai cewa rundunar ta samu kwato mutanen ne wanda suka hada da mata 180 da wasu ‘yan mata 129 da maza 127 da kuma dattawa 69.

Kwamandan yayi alkawarin ci gaba da kokarin ganin sun sake kubuto da sauran jama’ar dake hannun ‘yan Boko Haram.

Ranar takwas ga wannan wata runudnar sojan sunyi arangama da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram cikin dare, inda suka sami nasarar kwato makamai masu yawa da kuma hallaka mutane biyu daga cikinsu. Cikin wannan ranar ne rundunar ta sake shiga cikin dajin Sambisa inda ta hallaka wasu mayakan Boko Haram guda biyar.

Bisa ga bayanan sirri da rundar ta samu ta cafke wasu ‘yan Boko Haram, wanda yanzu haka ana ci gaba da yi musu bincike.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG