Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Raya Afirka Zai Bunkasa Kogunan Jama'are da Yobe


Ginin Hedkwatar Bankin Raya Afirka dake Abidjan babban birnin Ivory Coast
Ginin Hedkwatar Bankin Raya Afirka dake Abidjan babban birnin Ivory Coast

Bankin zai kashe zunzurutun kudi fiye da Euro miliyan biyu domin bunkasa kogunan Jama'are-Hadeija da kuma na Makomadugu-Yobe

Bankin ya dauki matakin ne saboda yadda sauyin yanayi ya shafi madafin ruwa a wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya, musamman na Chalawa da Tiga dake jihar Kano da haka ya kawo raguwar ruwan dake zuwa jihohin Yobe da Borno kuma hakan na shafar rayuwar al'ummar yankin.

Tuni har wasu kwararru daga kasar Australia suka isa Najeriya domin soma aikin gadan-gadan.

Ministan albarkatun ruwan Najeriya Injiniya Suleiman Useni Adamu yayi karin bayani akan shirin. Shirin zai raya Madugu Yobe kana zai shafi jihohi shida da suka hada da Kano, da Jigawa da Yobe da Borno da Bauchi da Filato. Za'a fito da abubuwan da suka shafi harkokin aikin noma da wasu bukatu da zummar inganta rayuwar mutanen yankin..

Dr. Hussaini Hassan na hukumar arewa maso gabashin Najeriya kwararre akan sha'anin koguna yace aikin tun daga sama za'a faroshi. Yace a jihar Jigawa akwai ruwa da suka kwanta a kasa basa kwarara domin wasu wayoyin daji da suka hanasu zuwa inda ake bukatarsu. Irin wadannan shirin zai kawar dasu ya bude hanyoyin ruwan.

Samun ruwa shi ne zai inganta noma a arewa saboda haka samun ruwan yana da mahimmanci ga manoman arewa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG