Yankin Madagali na cikin yankunan dake fama da wannan matsalar, inda yan Boko Haram suka lalata fiye da rijiyoyin burtsatse 160, lamarin da ya jefa al'ummomin dake komawan cikin wani mawuyacin hali.
Dan majalisar Dokokin jihar Adamawa mai wakiltar Madagali, Hon Imanuwa Tsandu, yace yanzu haka suna aikin tona rijiyoyi 40 domin samun warware matsalar ruwan sha, ya kuma tabbatar da cewa akwai rijijoyin burtsatse har 160 da aka lalata a yankin.
Baya ga matsalar ruwan sha yanzu haka kuma ana samun matsalar karancin motocin sufuri, sakamakon karancin Mai da ake fuskanta a wadannan wurare, hakan yasa hadakar kungiyar dillalan Mai a Najeriya, IFMAN, ta mika kukansu ga hukumomin tsaro da a sassauta talalar da aka saka a wadannan yankuna da aka kwato da ma garuruwan dake bakin iyaka.
To sai dai kuma ya zuwa yanzu kuma tuni fa kwamitin da shugaba Buhari ya kafa na tallafawa al’umomin da rikicin Boko Haram ya shafa karkashin tsohon ministan tsaro Janal TY Dan Juma da Alhaji Aliko Dan Gote suka fara aiki.
Your browser doesn’t support HTML5