Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kirga Kuri'u A Jamhuriyar Nijar


Zaben Nijar
Zaben Nijar

An fara kirga kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da aka gudanar a jamhuriyar Nijar bayan rufe runfunan zabe jiya Lahadi. Mai yiwuwa ba za a fitar da sakamakon zaben ba sai mako mai zuwa.

Shugaba Muhammadu Issoufou yana neman wani wa’adin mulkin shekaru biyar tare da alkawarin murkushe mayaka masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama, ya kuma bunkasa kasar da ta kasance daya daga cikin mafiya talauci a duniya.

Yace, “ina fata za a gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da lumana.”, yace a karshe duka, mai nasara guda ne, kuma ita ce Nijar.

‘yan takarar shugaban kasa goma sha hudu suka fafata da Mahammadou Issoufou, da suka hada da Seyni Oumarou, shugaban hadakar kungiyar hamayya.

Oumarou yace, “ mutum yana jin kamar an cimma wani buri ne a tsarin zaben. Zaben shine mataki na karshe, mun kuma hakikanta cewa, Allah zai taimakemu yau, yadda za a ci gaba da gudanar da wannan zaben shugaban kasar cikin kwanciyar hankali da lumana yadda dantakarar da yafi dacewa zai lashe zabe.”

Sauran ‘yan takarar hamayya sun hada da Hama Amadou, wanda aka tsare bisa zargin safarar jarirai.

Masu tsokaci kan lamura sun ce Issoufou na amfani da karfin siyasa kafin lokacin zabe, yana kakkama magoya bayan ‘yan hamayya, da ‘yan siyasa da manema labarai har da mawaka da suka fitar da wakokin da suke sukarsa.

XS
SM
MD
LG