Mista Juta, ya yi wannan furucin ne a wani taron manema labarai a birnin Tarraiyya Abuja. Bayan da wakiliyar Muryar Amurka, Madina Dauda, ta tambayeshi ko menene dalilin taron? Yace, abinda ya faru game da zaben shugaban jam’iyyar PDP ta Najeriya, ba a bi ka’ida ba, domin an bayar da wannan mukami ne a Kudu maso Gabashin Najeriya, inda tsohon shugaba Mu’azu ya fito domin a maye gurbinsa sai gashi an baiwa mutumin da bai kamata ba.
Ko wacce jiha a yankin ta kawo sunayen yan takarar da suke so, banda jihar Taraba wanda suka ce basa bukata, sauran jihohi biyar sun fitar da sunaye. Ana tsammanin cikin sunayen ne za a zabi shugaban jam’iyyar, sai gashi an kawo mutumin da ba a san kowaye ya kawo shi ba an bashi wannan matsayi.
Ganin cewar Sanata Ali Modu Sharif bai dade a cikin jam’iyyar ba, hakan ne yasa wasu jigogin jam’iyyar ke cewa basu san yadda akayi ya samu wannan kujera ba. Mista Juta dai yace tunda yake kowa ya sani ba a amince da abinda ya faru ba, don nema suka yi kira ga duk kwamitocin jam’iyyar da a zauna domin samar da masalaha.
Saurari hirar Madina Dauda da Wilberforce Juta.