Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yiwa iyalan wani dan kasuwa yankan rago a Birnin Kebbi


Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya
Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya

Yau a Birnin Kebbi aka wayi gari aka ga cewa wasu sun shiga gidan wani Shehu Dan Dare wanda ya yi tafiya suka yiwa iyalansa yankan rago

An kashe duka iyalansa guda biyar ta hanyar yankan rago tare da wasu 'ya'yan makwafta da suka da suka kwana gidan.

Mai gidan Malam Shahu Dan Dare dan kasuwa ne kuma yayi tafiya zuwa Onitsha. Wasu da ba'a san ko su wanene ba suka haura gidan suka yanka matarsa da duka 'ya'yansa.

Wani makwafcin gidan yace sun tashi da safe sun ga yara basu fito sun tafi makaranta ba. An buga gidan ba'a ji amsar kowa ba. Kanin matar ya hau katanga ya shiga gidan ya fito a rikice bisa abun da ya gani.

Da aka shiga gidan sai aka tarar an yaka duk wadanda ke cikin gidan . Ita matar bayan an yankata sai aka daddatseta. Abun ya haddasa tashin hankali.

Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin rundunar DSP Nasiru Abubakar ya bayyanawa manema labarai. Matar da aka yanka sunanta Amina mai shekaru 36 da danta Abdulhamid Shehu mai shekara uku da diyarta Hamida Shehu mai shekara uku. Akwai kuma 'ya'yan makwafta biyu. Akwai Aisha Rabiu 'yar shekara 17 da Nafisa Rabiu 'yar shekara tara. Duka aka yankasu.

Yanzu dai 'yansanda sun shiga bincike da zummar zakulo wadanda suka aikata wannan ta'asar. Abun mamaki shi ne ba'a dauki komi a gidan ba ba'a kuma cire komi daga cikinsu ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG