Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PNDS ta lashe zaben Nijar a jihohin Rivers da Edo


Nijar
Nijar

Sakamakon zaben kasar jamhuriyar Nijar a jihohin Rivers da Edo sun nuna jam'iyyar PNDS Tarayya ce ta lashe.

Jam'iyyar shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ita ce ta zamo ta daya a jihohin yayin da ta Hama Ahmadu MODEL Lumana ta zamo ta biyu.

Yayinda 'yan jam'iyyar PNDS ke farin cikin nasarar da suka samu su kuwa na jama'iyyar MODEL Lumana kaddara suka runguma tare da cewa haka Allah ya so. Amma suna kyautata zaton zasu samu nasara da zata sa kai Hama Ahmadu fadar gwamnati daga kurkuku inda yake yanzu

Wani dan jam'iyyar MODEL Lumana yace duk da magudin da jam'iyyar dake mulki ke yi su ne zasu ci nasara kamar yadda suka samu a Lagos da wasu wuraren a cikin Nijar din kanta.

Wadanda suka jefa kuri'u sun ce idan zabukan sun gudana kamar yadda suka yi nasu to za'a yi adalci saboda haka duk wanda ya fadi ya rungumi kadara. Sun bayyana irin ayyukan da suke so gwamnati ta yi masu kama daga gina hanyoyi zuwaa samar da ruwan sha .

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG