Mayakan Boko Haram sun kai wani wawan hari a sansanin sojojin Najeriya dake garin Rann cikin jihar Borno.
'Yan Boko Haram din sun fatattaki sojojin suka kashe na kashewa kana suka sace wasu ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaban gidauniyar Smile Medical Care Foundation dake tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, Dr. Sale Abba ya yiwa Muryar Amurka karin bayani.
A cewarsa ba zato ba tsammani aka rage jami'an tsaro sai da yamma aka fara jin harbe harbe a cikin barikin sojojin dake garin. Ya ce sojojin basu ankara ba kawai kwatsam sai suka ji ana yaren Kanuri. Daga nan sojojin suka sani mayakan Boko Haram sun kewaye barikinsu.
Inji Dr. Abba da lamarin ya fi karfin sojojin sai suka gudu zuwa cikin jeji. A cikin haka ne aka kashe mutane uku kuma daya daga cikinsu shi ne Dr. Kachi. Shi ne likita na bakwai da kungiyar Boko Haram ta kashe a yankin. Baicin kashe shi Dr. Kachi 'yan Boko Haram din sun sace wasu masu jinya, wato nurses guda uku, Hauwa Mohammed da Safina da Halima Muhammad wadda ta buga waya a daidai lokacin da 'yan Boko Haram din ke kokarin saceta.
Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kakakin sojojin Birgediya Janar Chukwu amma ba ta ci nasara ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5