Boko Haram Na Samun Horo Daga Kungiyar ISIS - Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da ya ke ganawa da VOA.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi ikrarin cewa kungiyar Boko Haram na samun horo daga kungiyoyin Islama da ke Gabas ta Tsakiya. Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da VOA.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce mayakan kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a kasar sun tafi Gabas ta Tsakiya domin neman horo a hanun mayakan Islaman yankin.

Ko da ya ke Jontahan bai ambaci kasar da mayakan na Boko Haram su ka je neman horon ba, amma a wata ganawa da VOA da ya yi a ranar laraba, shugaba Jonathana ya ce ya dade ya na kyautata zaton cewa mayakan suna da alaka da kungiyoyi masu ta da kayar baya na kasashen waje.

“Mu na da sanin cewa akwai alaka, ko da ya ke ba mu da masaniyar karfin dangantakar kungiyar da sauran kungiyoyi ba musamman ma ta fuskar irin tallafin da su ke samu da kuma irin makaman da su ke samu daga gare su da kuma mayakan kasa da kasa da su ke tallafa musu.” Jonathan ya ce.

Ya kuma kara da cewa “akwai wasu daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram da ke zuwa su samo horo daga ‘yan kungiyar ISIS su koma gida.”

MUGGAN HANYOYIN TA DA KAYAR BAYA

Tun a shekarar 2009 Najeriya ke yakar ‘yan kungiyar musamman ma a arewa maso gabashijn kasar, inda dubban mutane su ka rasa rayukansu, wasu su ka jikkata yayin da aka raba wasu da dama da muhallansu.

Daga cikin salon yakin da kungiyar ke amfani da su akwai harin kunar-bakin- wake da kuma yin dai-dai da kauyuka.

Kusan shekara guda ke nan da mayakan na Boko Haram su ka kai hari wata makarantar mata a garin Chibok, su ka yi garkuwa da sama da dalibai 200 wadanda har yanzu ba a jin duriyarsu.

Yanzu haka shugaba Jonathan na neman a sake zaben shi a wa’adi na biyu a zaben da za a yi a ranar 28 ga wannan wata na Maris.

Da yawa na kallon wannan zabe a matsayin mafi kalubale a duk zabukan da Najeriya ta taba gudanarwa tun bayan maido da tsarin mulkin dimokradiya.

A ranar 14 ga watan Aprilu ya kamata a gudanar da zaben, amma hukumar da ke da alhakin gudanarwa ta matsar zuwa gaba saboda jami’an tsaro sun ce babu isashun dakarun da za su samar da tsaro a lokutan zabe.

Tun daga wannan lokaci, sojojin Najeriya tare da na kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da ke makwabtaka da kasar, su ka fara kwato wasu garuruwa da mayakan sa kai su ka kwace a baya a arewa maso gabashin kasar.

Har ila yau a tattaunawar da ya yi da VOA, shugaba Jonathan ya dora alhakin wannan nasara da aka samu akan hadin gwiwar dakarun makwabta da na Najeriya da kuma sabbin makamai da aka baiwa dakarun kasar.

MAYAR DA MARTANI

Shugaba Jonathan ya kuma maida martani ga wadanda su ke ikrarin cewa an hana dakarun kasashen waje su kutsa kai a yankunan da ke hanun Boko Haram a Najeriya.

Ya kuma kara da cewa da farko kasar Kamaru ta ki amincewa Najeriya ta kutsa kai cikin kasarta domin farauto ’yan kungiyar ya na mai cewa hadin gwiwar dakaru abu ne da ke bukatar tsari.

“Ina ga wannan batu---duba, ya kamata mu gane duk wani babban kalubalen tsaro, ya kamata a ce sojojin Najeriya su kasance tare da kai.” Shugaban ya ce.

A cewar Jonathan, yanzu haka akwai kwararru da ke horar da sojojin Najeriya kan yadda za su yi amfani da sabbin makaman, tun da babu lokacin da za a horar da su kafin a kai su filin daga.”

“Saboda haka, muna da wadannan kwararru da ke horar da dakarun kan yadda za su yi amfani da sabbin makaman da kuma kwararru da za su dinga gyara makaman tare da horar da mutanen mu kan yadda za a kula da makaman.”

Shugaban Jonathan ya kuma ce kwararru an samo su ne daga wasu kamfanoni guda biyu, amma ya gujewa ambatar sunayen kasashen da kamfanonin su ka fito.

Haka zalika, shugaba Jonathan ya kore ikrarin da wasu ke yi na cewa matsalar Boko Haram ita za a fi tunawa a lokacin mulkinsa.

“Lallai babban kalubale ne ta fuskar tsaro, kuma ya na sahun gaba a matsayinmu na kasa, amma ba a mana adalci ba idan aka kalli wannan matsala aka yi mana fassara.”

Yayin da dakarun hadin gwiwa ke ci gaba da fafatawa da mayakan kungiyar ta Boko Haram, shugaba Jonathan ya ce nan da tsakiyar mako mai zuwa za a yi galaba akan su.

Ya kuma kara da cewa za a kakkabe ‘yan kungiyar nan da makwanni uku ma su zuwa jahar Borno da mayakajn su ke da tushe.

Sai dai duk da haka, ya ce akwai yuwuwar a ci gaba da samun karin hare-hare a kasuwanni da tashoshin mota yana mai cewa matakin da gwamnati ke shirin dauka shi ne a kara tsaurara matakan tsaro ta hanyar tattara bayanan sirri tare da samar da ayyukan yi da karfafa hanyoyin samar da ilimi a arewa maso gabashin kasar.

BUHARI YA YABAWA DAKARU

A wata hira da ya yi ta daban da VOA, Babban abokin hamayyar shugaba Jonathan, Janar Muhammadu Buhari, ya ce bai yi mamaki ba da ya ga sojojin Najeriya na samun galaba akan ‘yan kungiyar Boko Haram.

A cewarsa, tun da farko ne ba a baiwa dakarun makamai na kwarai ba kana ba a karfafa musu gwiwa ba ya kara da cewa hadin gwiwar da aka samu da makwabta irinsu Chadi da Nijar da Kamaru ne ya tilastawa gwamnati ta samar da makamai masu nagarta ga dakarun na Najeriya.

Ya kuma jinjinawa dakarun Najeriya wadanda ya ce sun yi fice a fannin samar da zaman lafiya a duk fadin duniya ya kuma yi musu alkawarin kyautata musu idan har ya yi nasara a zabe.