Birtaniya Za Ta Inganta Aikin 'Yan Sandan Kano

jami'an 'yan sanda

Hukumar raya kasashe ta Birtaniya, DFID, za ta gina ofisoshin 'yan sanda na zamani a wasu sassan jahar Kano
Nan kusa shirin “Justice for all Program” na hukumar raya kasashe ta kasar Birtaniya DFID zai gina ofisoshin ‘yan sandan da za’a sanyawa kayan aikin zamani a yankuna biyar na jahar Kano domin kyautata mu su ayyukan su. Yankunan da za a samar da wadannan ofisoshin ‘yan sandan su ne Farm Center, da Hotoro, da Bampai, da Sabongari da kuma garin Wudil. Malama Aisha Abakar jami’ar ofishin hukumar DFDI mai kula da shirin na “Justice for all Program” a shiyar maso yammacin Najeriya ta shaidawa wakilin Sashen Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari cewa an kammala shirye-shiryen kama aikin gadan-gadan:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar raya kasashe ta Birtaniya za ta inganta aikin 'yan sanda a Kano - 2:35