Maharan da suka yi awon gaba da attajirin sun harbi mutum guda wanda tuni aka kaishi asibitin Gwagwalada inda yake karban magani. Lamarin da ya faru ranar Lahadi bayan sallar isha'i ya tayar da hankalin mutanen anguwar. Kawo wannan lokacin babu labarin inda aka nufa da wannan dan kasuwa.
Malam Mohammad Sani makwafcin Alhaji Umar Maikwarya ne ya ce wasu mutane ne suka biyo shi gida bayan ya yi sallar isha'i suka kama shi kana suka harba bindiga wadda ta samu wani bawan Allah dake kusa da wurin. Ya ce kawo lokacin da yake magana babu wani labari game da wanda aka sacen. Lamarin, inji shi, ya faru ne misalin karfe bakwai da rabi.
An kaima jami'an tsaro rahoton abun da ya faru. Don haka ita ma rudunar 'yansandan jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin. Kakakin 'yansandan Mr. Richard Adamu ya ce sun samu rahoto amma basu da wani labari har yanzu. Ya ce an fada masa an kinkimoshi an sashi a mota amma babu wanda zai ce ga irin motar ko launinta ko dai yadda ta ke. Sai dai rundunar ta ce tana kan maganar domin satar mutane a Najeriya ya zama ruwan dare gama gari.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.