Jami’ar shirin na Justice For All a Arewa maso yammacon Nijeriya Hajiya A’isha Abubakar ta ce irin taimakon da su ke bayarwa ga bangaren na shari’a sun hada har da ankarar da bangaren na shari’a idan ya kauce hanya; akwai kuma tallafin kudade da kayan aiki da sauransu.
Malama A’isha ta gaya ma wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari cewa wani sa’in kuma hukumar kan hada hannu da bangaren na shari’a wajen shirya wasu abubuwan amfanar da jama’a game tsarin doka da dai sauransu.
Wakilin na mu ya kuma ruwauto wani dan Majalisar Dokokin jihar Kano mai suna Hon Gambo Sallau na cewa Majalisar ita ma za ta kwaskawre bangaren na shari’a saboda adalci ya kankama a jihar.
Shi ma Attoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ar jihar Kano, Barrister Maliki Kuliya Umar, y ace Ma’aikatar Shari’ar Kano za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma wadannan gurorin.