A yau Litinin Frayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yana da yakini kasashen turai za su maida ofisoshin jakadancinsu zuwa birnin kudus.
Ya kuma ce yana fatan za su dauke shi a matsayin babban birnin na Isra'ila, biyo bayan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na shirin aiwatar da hakan.
Yayin da yake magana a birnin Brussels a gefen shugabar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta EU, Federica Mogherini, Netanyahu ya ce hakan da Trump ya yi ya fito fili ne da bin da yake a bayyane.
Ya kara da cewa da ma ginshikin cimma zaman lafiya, shi ne aiki da abin da yake na zahiri.
Sai dai Mogherni ta ce kungiyar tarayyar turai za ta ci gaba da bin yarjejeniyar kasashen duniya akan birnin na Kudus har sai an sasanta lamarin, kalaman da ke nufin ba sa tare da hukuncin da Trump ya yanke.
Moghernin ta kara da cewa "maganin da zai kawo zaman lafiya a kasashen Isra’ila da Falasdinu shi ne a saka birnin na kudus a matsayin babban Birnin Isra’ila da Falasadinu.”