Shugaban kungiyar kasashen Larabawa yayi kira ga kasashen duniya da su amince da Falasdinu a matsayin ‘kasa mai ‘diyauci da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar, a wani martani da ya bayar bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, kuma za a mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa can.
Ahmed Aboul-Gheit yayi wannan kira ne jiya Asabar lokacin wani taron gaggawa da ministocin harkokin kasashen waje na kasashen Larabawa suka gudanar. Ya kara da cewa wannan shela da Amirka ta yi tamkar amincewa ne da mamayar da Yahudawa su ka yiwa Falasdinu.
Ya kuma ja ayar tambaya kan matsayin Amirka na mai taka rawa wajen kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya dama duniya baki ‘daya.
Wasu jami’an diplomasiyya daga kasashen Larabawa, sun bayar da shawarar a rubuta takarda ga kwamitin sulhu na MDD ta yin Allah wadai da shawarar da Amurka ta yanke.
Taron gaggawar da aka gudanar jiya Asabar a birnin Cairo, ya zo ne bayan kwashe kwanaki uku ana zanga-zanga kan tituna a yammacin kogin Jordan da zirin Gaza, da kuma zanga-zangar da aka yi a masallacin Al-Azhar.
Facebook Forum