Yau lahadi kasar Iraqi tayi faretin a babban birni kasar, na samun nasara akan kungiyar IS.
Wannan ko yana zuwa ne kwana bayan da Prime Ministan kasar Haider Al-Abadi ya bayyana nasarar korar kungiyar IS daga cikin kasar.
Sai dai ba a dauki wannan faretin kai tsaye ba a kafofin yada labarai ba, sai dai kafar yada labarai mallakar gwamnati ce kawai aka bari ta halarci wurin.
Wadanda suka samnu damar kallon faretin sun bayyana cewa sojojin na Iraqi sunyi faretin ne a inda suka gitta babban dandalin dake tsakiyar cikin babban birnin kasar, yayin da jirage masu saukar ungulu aka gansu suna shawagi.
A cikin shafin sa na Twitter, Prime MInistar Abadi ya godewa sojojin kasar ta Iraqi na wannan abinda ya kira namijin kokari, kana yace suma wadanda suka mutu a fagen fama ba za a manta dasu ba.
Yanzu haka Abadi ya ayyana yau lahadi a matsayin ranar hutu ga kasar,
Tun jiya ne Prime MInistan ya bayyana cewa yakin da aka kwashe shekaru 3 anayi an samu damar korar yan kungiyar IS daga cikin kasar ta Iraqi, anyi nasara akai kuma an kawo karshen yakin Kenan.
Facebook Forum