Kungiyar tarayyar Larabawa tace matsayin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na amincewa da birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin kasar Iszaela abu ne dake cike da hadari, da kuma nuna son zuciya ga Amurka wanda ke nuna kaucewa dokokin kasa da kasa.
Wannan sanarwan dai ta fito da safiyar yau lahadi bayan da kungiyar ministocin harkokin waje ta kamala wani taron gaggawa da tayi a Cairo.
Kungiyar tace wannan matsayi da shugaba Trump ya dauka ya tubewa Amurka matsayin ta na mai kokarin ganin an samu maslaha a kasashen gabas ta tsakiya.
Haka kuma taron ya bayyana cewa wannan matakin ya kara sukurkuta kokarin ganin samar da zaman lafiya wanda hakan zai kara ruruta wutar kiyayya da zai ingiza yankin cikin wani sabon munanan tashe-tashen hankula.
Akan haka ne shugaban kungiyar kasashen na Larabawa yayi kira ga kasashen duniya dasu dauki kasar Falesdinu a matsayin kasa mai diyauci kamar yadda birnin Kudus take babban birnin Iszaela, a sakamakon sanarwan da shugaba Trump ya bayar.
Daga karshe taron Ministocin ya bukaci Kwamitin sulhu na MDD da ya samar da wani kudiri da zaiyi ALLAH Waddarai da wannan shawarar ta Shugaba Donald Trump.
Facebook Forum