A yau jumma’a, 'Yan sandan Isra'ila sun harba barkonon tsohuwa a kan 'yan zanga-zangar Falasdinawa a garin Bethlehem, a yayin da aka kaddamar da ranar nuna fusatar da sassan na Falasdinawa suka bukaci a yi.
An tura karin 'yan sanda da dakarun tsaro zuwa Birnin Kudus biyo bayan sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump yayi, ta ayyana cewar birnin na Qudus shine babban Birnin Isra’ila kuma Amurka na shirin mayar da ofishin jakadancin ta can.
A can baya, Isra'ila tana hana matasa shiga Masallacin al-Aqsa na Qudus a inda tashin hankali ke barkewa a duk lokacin zaman tankiya. Mai Magana da yawun yan sanda israila Mickey Rosefeld yace “ ba mu ga wasu alamun tashin hankali a wurin ibadar ba, don haka ba mu kayyade shekaru ba. Idan wani abu ya tashi, zamu dauki mataki cikin gaggawa.
Wannan Masallaci na al-Aqsa shine na uku wajen tsarki ga Musulmi, yayin da yankin wurin shine mafi tsarki ga Yahudawa, wadanda suke kiran shi Temple Mount.
A yau jumma'a, ana zanga-zanga a fadin Gabas ta Tsakiya da kasashen da Musulmi ke da rinjaye.
Dubban mutane sun yi gangami a kofar ofishin jakadancin Amurka dake Kuala Lumpur, babban birnin Malaysia. Wasu daga cikin 'yan zanga-zangar suna dauke da kwalayen dake yin tur da shugaba Donald Trump, wasu kuma na cewa "dage hannu daga kan Qudus."
A Indonesiya, kasar da ta fi yawan Musulmi a duniya, daruruiwan 'yan zanga zanga sun yi cincirindo a kofar ofishin jakadancin Amurka a Jakarta, suna cewa "Trump ya haukace" "mutuwa ga Trump."
Facebook Forum