Bill Gates Da Dangote Sun Yi Rangadi A Nijar Inda Suka Gana Da Shugaba Bazoum

Bill Gates da Dangote sun yi rangadi tare da shugaba Bazoum

Shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates, wato attajirin nan na kasar Amurka, Bill Gates da  attajirin Najeriya kuma shugaban gidauniyar Dangote Foundation, Aliko Dangote sun yi rangadi a jamhuriyar Nijar yau Litinin 19 ga Yuni, 2023 inda suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa.

Shugaban gidauniyoyin Bill da Melinda Gates Foundations attajirin kasar Amurka Bill Gates ya yi jawabi jim kadan bayan ganawa da shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum a yayin ziyarar da suka gudanar a wannan Litinin a birnin Yamai a wani bangare na rangadin da ya Kawo shi Najeriya da Nijar. Batun kiwon lafiya musamman na shaushawar riga kafin cutar Polio ne ke gaban abubuwan da aka tattauna kansu a yayin wannan haduwa, kasancewar Nijar na daga cikin kasashen da ke morar ayyukan da Bill da Melinda Foundations ke gudanarwa.

Bill Gates da Melinda Gates

Fitaccen dan kasuwar Najeriya kuma shugaban gidauniyar Dangote Foundation Alhaji Aliko Dangote ya yi karin haske game da abinda aka saba gaba. Ya ce suna so su tabbatar da kiwon lafiya a Nijar da ma Najeriya baki daya musamman kan cutar shan inna.

Aliko Dangote

Jajircewar hukumomin Nijar akan maganar kiwon lafiya da yadda kasar ta yi fice a ‘yan shekarun akan maganar allurar riga kafi a baki dayan yankin Afrika ta yamma ya sa shugabannin wadanan Gidauniyoyi Bill da Melinda da ta Dangote yin tattaki zuwa wannan kasa domin jinjina masu.

Bill Gates da Dangote sun yi rangadi tare da shugaba Bazoum

A watan oktoban 2022 ne Nijar ta shirya taron shugabannin kasashe kan maganar allurar riga kafi wanda a karshensa mahalartan suka sha alwashin karfafa ayyukan shaushawa.

Bill Gates da Dangote sun yi rangadi tare da shugaba Bazoum

Watannin 5 bayan gudanar da wannan taro Bill da Melinda Foundations da Dangote Foundation sun cimma yarjejeniya da gwamnatin wannan kasa domin karfafa ayyukan allurar riga kafi a jihohin Diffa da Zinder da Maradi, abin da ya sa kenan a yayin rangadin na wannan litinin 19 ga watan yuni, aka yi zaman bita da ya hada Bill Gates da Aliko Dangote da a daya gefe mukarraban gwamnati a karkashin jagorancin Fra minister Ouhoumoudou Mahamadou.

Bangarorin sun kuma tattauna akan hanyoyin da za a bullo wa wasu matsalolin na daban da suka addabi Nijar wadanda suka hada da ta’addanci, canjin yanayi da bunkasar yawan al’umma ba kakkautawa a wani lokacin da yawan ‘yan gudun hijirar cikin gida da na waje ya haura 650000.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

ZIYARAR BILL GATES A NIJER .mp3