An samu raguwar mutuwar mata da jarirai a wajen haihuwa, daga 1,575 cikin haihuwa 10,000, zuwa 800 a gombe, a cewar hukumar lafiya matakin farko ta gombe.
A taron kammala aikin tallafi na tsawon shekaru 10 da asusun GATES da MELINDA su ka gudanar a wasu jihohin arewa, hukumar lafiya ta jihar Gombe ta ce, an samu raguwar mutuwar mata da yara a jihar da kimanin rabin adadin rashi na 1,575.
Taron bitar nasarori da kalubalen aikin tallafin da a ka gabatar a Abuja, ya bayyana cewa, a baya a jihar Gombe kadai a kan samu mutuwa 1,575 cikin haihuwa 100,000 inda a halin yanzu lamarin ya ragu zuwa 800.
Darakta a hukumar lafiya matakin farko ta jihar da ke tsakiyar arewa maso gabas, Muhammad Kolo Bagoja ya ce, nasarar wayar da kai daga tsohuwar dabi’ar kin jinin zuwa asibiti ya taimaka ainun wajen rage asarar rayukan mata da jariran.
Bayan kammala wannan shiri, babban sakataren hukumar Dr. Abdulrahman Shu’aibu ya ce, an gudanar da aikin a gundumomi 57, kuma ba’a fuskanci kalubale mai tsanani ba.
Asusun Bill da Melinda daga miji da mata da ke cikin mafiya yawan kudi a duniya, na ware miliyoyin dala duk shekara don tallafawa kasashe masu tasowa ga yaki da cututtukan ciki da shan inna.
“A lokacin hutu da mu ka tafi Afirka mu na tafiya a bakin teku a nan ne mu ka dau alwashi za mu ba da tallafin mafi yawan dukiyar da mu ka samu daga kamfanin manhajar MICROSOFT ga al’umma” inji Melinda Gates a zantawa da gidan talabijin na CBS kan aiyukan asusun a kasashen duniya.
Bill Gates ma ya ba da tabbacin faruwar hakan da karawa da yadda su ke kaunar taimakawa lafiyar yara.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka daga Abuja, Nasiru Adamu El-hikaya.
Facebook Forum