Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bill Gates Da Matarsa Melinda Sun Rabu Bayan Auren Shekara 27


Bill Gates da matarsa Melinda a shekarar 2019.
Bill Gates da matarsa Melinda a shekarar 2019.

“Muna bukatar sirri a daidai wannan lokaci da iyalinmu ke kokarin fara wata sabuwar rayuwa.”

Gates, wanda da shi aka kafa kamfanin Microsoft, da matarsa, sun amince za su ci gaba da aiki tare a gidauniya mafi girma a duniya da suka kafa, wacce ake kira Bill & Melinda Gates Foundation.

Cikin wasu sakonnin Twitter iri daya da suka wallafa, sun ce sun amince za su kawo karshen aurensu da suka kwashe shekara 27.

"Mun reni ‘ya’ya uku, mun kuma kafa gidauniya wacce ke aiki a duk fadin duniya da zimmar ganin jama’a sun yi rayuwa cikin koshin lafiya da inganci,” sanarwar ta su ta ce.

“Muna bukatar sirri daga jama’a, a daidai wannan lokaci da iyalinmu ke kokarin fara wata sabuwar rayuwa.”

Sakon Twitter ya kara da cewa, "mun yanke wannan shawara ce, bayan aiki da zurfin tunani da muka yi, mun yanke shawarar mu kawo karshen aurenmu."

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG