Amurkawa na bikin Ranar Ma’aikata ta shekara- shekara a ranar Litinin da ke kira "Labor Day," wacce a hukumace ake jinjinawa ma’aikatan kasar, bikin da har ila yau yake nuni da zuwan karshen lokacin bazara – amma ba a hukumance ba
Bikin ya kawo karshen hutun karshen mako na kwanaki uku da mutane da yawa ke amfani da shi wajen kammala hutun karshe yayin da yara suka fara sabuwar shekara a makarantu.
Shagunan sayar da kayyaki kan yi amfani da wannan lokacin biki wajen karya farashin kayayyaki a sassan kasar.
Hukumar kula da sufuri a Amurka ta yi hasashen tantance mutum sama da miliyan 17 a filayen jiragen sama na kasar daga ranar Alhamis da aka fara hutun zuwa gobe Laraba da za a kammala a cewar Kamfanin Dillancin Labari na AP ya ce,
Wadanda ke tafiya da mota a lokacin hutun suna fuskantar matsakaicin farashin man fetur wanda ya yi kasa da kashi 10 cikin 100 kasa da irin wannan lokaci a bara.