Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Iyalen Amurkawa Sun Shiga Damuwa Bayan Dakatar Da Wani Shirin Zama 'Yan Kasa


Roberto Garcia and his wife
Roberto Garcia and his wife

Wan Mai Shari’a A Amurka Ya Dakatar Da Shirin Da Ke Baiwa Iyalan Amurkawa Iziznin Zama 'yan Kasa

Lauyoyin da suka kware akan al’amuran bakin haure sun ce iyalai sun shiga cikin damuwa bayan da wani mai shari’a a babban kotun Texas ya dakatar da wani shirin da gwamnatin Biden ta samar wanda zai baiwa iyalan Amurkawa damar zama ‘yan kasa.

Umarnin kotun da aka fitar a daren ranar Litinin ya biyo bayan da jihohi 16 suka kaliubalanci shirin wanda wani babban lauya dan Republican ya jagoranta.

Bakin haure akalla dubu 500,000 ne a kasar zasu amfana da shirin sannan da kuma akalla ‘yayansu su dubu 50,000.

Za a dakatar da shirin na tsawon kwanaki 14 sai dai kuma akwai yiwuwar a kara wa’adin dakatarwar. Hukumar kula da al’amuran bakin Haure ta ce gwamnati zata ci gaba da karbar takardun neman izinin zama ‘yan kasa yayin da take kokarin kare shirin a kotu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG