Ya yi kira ga ma'aikatan agaji da masana kimiyya da masu bincike da wadanda suka sadaukar da kansu domin Gwajin rigakafi da dakarun da zasu yi Kirsimeti bada iyalansu ba.
"Zukatanmu koyaushe suna tare da ku – a kiyaye imani," a cewar Biden a jawabinsa na karshen shekara daga garin Wilmington, na jihar Delaware.
Lura da yadda cutar ta sauya masa yadda ya saba yin bikin, wanda galibi ya kan hada da dangi har zuwa dozin biyu, Biden ya ce, "banda wannan shekarar."
Biden ya ce “wannan lokaci na tafakkuri na dauke da ma’ana mai zurfi fiye da irin wannan lokuta a baya, yana mai bada kwarin gwiwa ga Amurkawa su ci gaba da karbar rigakafin domin dakile yaduwar cutar da ta riga ta kashe mutum dubu 230 a Amurka. Ya ce “Ni da Jill muna addu’o’I kamar yanda na san ku kuma kuna yi zuwa mutanen dake cikin mawuyacin lokaci.”
A ranar Litinin ne dai Biden ya karbi na shi allurar rigakafin da aka nuno kai tsaye ta telbijin, domin tabbatarwa mutane cewa rigakafin COVID-19 bashi da matsala.