A yau Litinin ake sa ran majalisar dattawa da ta wakilan Amurka zata kada kuri’a akan kudurin bada tallafin rage radadin tattalin arziki da annobar coronavirus ta janyo na dala biliyan 900 wanda zai taimakawa Amurka da masu masana’antu.
Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka kwashe ana zaman shawarwari a lokacin da shugabannin jam’iyyar Democrat da Republican a majalisun suka sami sabanin ra’ayoyi akan yawan kudin tallafin da gwamnati zata bada, da kuma ko za a ba batutuwa kamar tallafin rasa aiki ko barin harkokin tattalin arziki su ci gaba da aiki fifiko.
Matakin kuma na zuwa ne yayin da ake samun karin masu kamuwa da cutar COVID-19, inda Amurka ta samu kusan mutane miliyan 18 da suka kamu da cutar, ana kuma samun fiye da mutane dubu dari 200 da ke kamuwa da cutar a duk rana. Adadin mace-mace a kasar kuma ya zarta 317,000, a cewar jami’ar Johns Hopkins.