Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Bai Dauki Batun Kutsen Da Rasha Ta Yiwa Amurka da Muhimmanci Ba-Democrat


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

An yiwa ‘yan majalisar dokokin Amurka bayani a kan gagarumin kutsen yanar gizo da aka kai a kan cibiyoyin gwamnatin Amurka, kana sashen masu zaman kansu na kira ga kasar ta tashi tsaye, kashedi da aka yi da bayanai da aka tattara na nuni da Rasha ce take wannan aiki.

Bayanan daga ‘yan Republican da ‘yan Democrat, sun fito ne daga kashedi da jami’an kula da tsaron yanar gizo na Amurka suka yi cewa girmar kusten ya zarce abin da ake tunani, saboda ya taba shafukan manhajoji da dama tun daga akalla watan Maris na shekarar bara.

Har yanzu ba a iya gane girmar harin kutsen da aka yi ba, amma muna sane da yana da matukar girmar da ba a taba gani irinsa ba, inji shugaba mai riko na kwamitin tattara bayanan sirri a majalisar dattawa, dan Republican Marco Rubio a wani sakon twitter a jiya Juma’a.

Hanyar da aka yi amfani da ita wurin kai harin kusten ya yi daidai da yanda Rasha ke ayyukan yanar gizo inji Rubio, yana kashedi cewa, tun da jami’ai sun tabbatar da inda kutsen ya fito, toh wajibi ne Amurka ta maida martani kuma kada ya tsaya ga takunkumi kadai.

Shugaban Democrat a kwamitin tattara bayananin sirri na majalisar dattawan, Sanata Mark Warner, kamar takwararsa ya bayyana fargaba a kan kusten da ya kwatanta da mai matukar muni.

Sanata Warner ya fada a wata sanarwa cewa irin wannan batu da mummunar tasirinsa ya yi girma, yana buakatar gwamnatin Amurka ta dauki matakin martani tare da jama’a. Ya ce lamarin nada matukar damuwa ganin shugaban kasa ya yi biris da batun, bai bada muhimmanci ga wannan batu mai girmar gaske.

XS
SM
MD
LG