Kokarin da Johnson ke yi na neman kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci ya faro ne daga wata hirar waya tsakanin shugabannin biyu da suka tabo abubuwa da dama a kan matakan da duniya ke dauka na yaki da annobar coronavirus da kuma sanarwar da gwamnatin Biden ta bayar a wannan mako cewa Amurka zata sake shiga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris da kuma komawa hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, a cewar sanarwa daga fadar firai ministan Birtaiya a Downing Street.
Sabuwar yarjejeniyar ciniki tsakanin manyan kawayen wani babban aiki ne da Johnson ya ba shi muhimmanci fiye da Biden. Birtaniya ta samu cikakken iko a kan shirin kasuwancinta ne a farkon wannan wata, bayan da ta cika sharudan ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.
Sakataren jarida a fadar White House Jen Psaki ta fada a ranar Juma’a cewa gwamnatin bata gindaya wani lokaci na kulla sabuwar yarjejeniya ba, yayin da Biden yafi maida hankali a kan yaki da annobar coronavirus da kuma matsawa majalisar dokokin Amurka lamba ta amince da shirin tallafin coronavirus na shugaban kasa na dala triliyan $1.9.
Hirar da Johnson shine akalla na uku da Biden ya yi da takwarorin sa na kasashen waje a ranar Juma’a. Shugaban ya kuma tattauna da firai ministan Canada Justin Trudeau da shugaban kasar Mexico, Andrés Manuel López Obrador da yammacin ranar Juma’a.