Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ka Iya Huskantar Jan Kunne Idan Majalisa Ta Same Shi Da Laifin Ingiza Tarzoma


Donald Trump
Donald Trump

A ranar Litinin ne kakakin majalisar wakilai Nanacy Pelosi zata aike da bayani a kan tsige Donald Trump zuwa majalisar dattawa inji shugaban ‘yan Democrat a majalisar dattawan Chuck Schummer a jiya Juma’a.

Wannan ne zai zama matakin farko na fara shari’a da ka iya sanadiyar hukunta tsohon shugaban kasar a kan ingiza mummunar tarzomar da ta lakume rayuka a majalisun Amurka.

“Lallai akwai shari’a”, Schummer yana fada a zauren majalisar dattawa. Ya ce “za a gudanar da cikakkiyar sharia.” Kuma za a yi shari’a ta gaskiya.”

‘Yan Democrat sun yi watsi da bukatar shugaban masara rinjayi a majalisar dattawa Mitch McConnelle na neman jinkirta shari’ar tsigewar har izuwa sabon wata, saboda lauyoyin Trump suna bukatar lokaci su shirya dabarun kare shi.

Trump shine shugaban Amurka na da aka tsige shi sau biyu kuma na farko da za a yi shari’a a kan sa bayan ya sauka daga mulki. Sai dai Schummeer bai ce ga ranar da za a fara shari’a a kan tsige Trump na biyun ba amma indai har an tabbatar ya aikata laifin ingiza tashin hankalin, za a haramta masa rike wani mukamin tarayya.

Tabbatar da laifi zai bukaci kuru’u 17 daga ‘yan Republican a majalisar dattawa amma ya zuwa yanzu ‘yan Republican kalilan ne suka nuna zasu amince da hukunta Trump kana galibi sun bayyana shakku a kan yiwa shugaban kasa shari’a bayan kammala wa’adin sa a dokance.

‘Yan Repblican sun kuma ce shari’ar zata kawo rarraba kana zata kawo tsaiko ga ayyukan sabuwar gwamnatin Biden.

Yayin da ake ci gaba da shirye shiryen fara shari’ar, Schummer da McConnelle tsohon shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa kafin Democrat ta kwace rinjayi da karamin rata a majalisar da ta yi kankankan, inda yanzu Democrat zata shige gaba saboda kuri’ar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris da zata raba gardama.

XS
SM
MD
LG