Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Gwamnatin Somalia Da Tura Sojojinta Zuwa Tigray Su Taimakawa Abiy


Sojojin Somalia
Sojojin Somalia

Ana kara matsawa gwamnatin Somalia lamba, yayin da ake zargi ta aika da sojojin Somalia din zuwa makwabciyar kasar Habasha domin su shiga mummunar yakin Tigray.

Iyaye mata sun yi wata zanga zangar da ba a saba gani ba a Mogadishu, babban birnin Somalia da ma wasu wurare suna buakatar sanin makomar ‘ya’yan su da a baya aka tura su domin basu horon soja a Eritrea.

Iyayen sun nuna damuwa cewa an kai ‘ya’yan su zuwa yankin Tigray, inda sojojin gwamnatin Habasha suke fada mayakan Tigray, tun cikin watan Nuwamba, a wani tashin hankali dake barazana ga zaman lafiyar yankin kuryar Afrika.

“Na ji cewa ‘ya’yan mu da aka tura su Eritrea domin basu horon soja, an dauke su aiki, kuma babban aiki da zasu yi shi ne taimakawa Firai minister Abiy Ahmed su yi masa yaki,” inji Fatuma Moalim Abdulle, mahaifiyar wani soja dan shekaru 20 Ahmed Ibrahim Jumale, tana fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press.

Ta ce “a wasu bayanai da na samu na nuna cewa, an kwashe ‘ya’yan mu kai tsaye zuwa garin Mekelle,” babban birnin yankin Tigray. Ta ce “zaka fahimci yanda nake a jiki na, ni uwa ce wacce ta yi kayan juna biyu tsawon watanni tara, dan haka jini da tsoka na ne.”

A wannan mako Habasaha ta musunta rahotanni dake nuni da sojojin Somalia na yankin Tigray, haka zalika take ci gaba da musunta babu sojoji Eritrea a wurin.

Abiy ya yi da zaman lafiya da makwabciya Eritrea a shekarar 2018, lamarin da a kai shi ga samun lambar yabon zaman lafiya ta Nobel Peace Prize.

Yanzu masu sukar lamiri sun ce Habasha da Eritrea sun hada kai a yaki da wadanda suke musu kallon abokan gaba, waton shugabannin yankin Tigray mai fama da tashin hankali, wanda gwamnatin Habasha ta mamaye kusan shekaru 30 kafin Abiy ya hau karagar mulki ya fara wani zagaye na tattaunawar zaman lafiyar yanki da ta hada da Somalia.

Shugaban kwamitin majalisar dokoki a kan harkokin kasashen waje Abdulqadir Ossoble Ali, ya yi kira ga shugaban Somalia Abdullahi Mohamed Abdullahi da ya gudanar da bincike a kan zargin shigan sojojin Somalia a yakin Tigray.

XS
SM
MD
LG