An yi ta hasashen cewa su biyun za su yi nasara, amma an sa ido sosai kan tazarar nasarorin a matsayin alamun nuna goyon baya ga ƴan takarar biyu a babbar jihar, gabanin sake fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa irin na shekarar 2020 wanda Biden ya lashe.
Yayin da aka kammala tattara kashi daya bisa uku na ƙuri'un da aka kirga a zaɓen shugaban ƙasa na Dimokarat, Biden na kan gaba da 80%, yayin da 14% na masu zaben sun kada kuri'ar "ba ruwa na."
Jihar Michigan dai ita ce jiha mai mafi yawan Larabawa Amurkawa a cikin kasar, kuma adawa da goyon bayan da Biden ke bai wa Isra'ila yakin da ta ke yi a Gaza da mayakan Hamas ya sa wasu 'yan Demokrat kira ga masu jefa kuri'a su kada kuri'ar "ba ruwa na" maimakon jefa kuri'a ma Biden.
Magoya bayan kokarin da aka yi na kada kuri'un "ba ruwa na" sun ce suna fatan samun kuri'u 10,000 irin wannan, matakin da ya fi sauki. Yayin da aka kidaya kusan kashi daya bisa uku na kuri'un, an riga an sami kuri'u sama da 38,000 na "ba ruwa na".
A zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Trump na kan gaba kashi 66% na kuri'un da aka kada idan aka kwatanta da kashi 28% na tsohuwar gwamnan jihar South Carolina Nikki Haley.
Trump ya yi nasara a wannan muhimmar jihar fafatawar siyasa a zaben kasa na 2016 a nasarar da ya yi na neman shugabancin kasar, amma Biden ya doke shi a 2020, wanda ya taimaka masa ya dakile yunkurin Trump na sake cin zabe.
Haley dai ta ci gaba da zama a gasar duk da cewa ba ta lashe ko daya daga cikin jihohin da aka fafata ba kawo yanzu. Ta kafa hujja da cewa masu jefa kuri'a na Amurka ba sa son sake karawa tsakanin Biden da Trump a zaben Nuwamba kuma idan hakan ya faru, Trump zai sha kaye a karo na biyu a hannun Biden.
Haley ta ce za ta ci gaba da gwabzawa har zuwa a kalla gasar da ake kira Super Tuesday da za a yi ranar 5 ga Maris wadda ta kunshi jihohi 15, yankuna biyu da kashi daya bisa uku na daukacin wakilan da ke kan gaba a zaben na Republican.