Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Shugaban Amurka Joe Biden Ya Fara Tiktok


Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden
Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya shiga TikTok a ranar Lahadin da ta gabata, inda a karon farko ya wallafa wani bidiyo na dakika 26 a kafar sada zumuntar ta Tiktok.

Matakin ya biyo bayan shafe lokuta da dama da sukar da gwamnatin Amurka ta yi kan dandalin na sada zumunta ta hanyar wallafa bidiyo a shekarun baya-bayan nan, musamman daga 'yan jam'iyyar Republican harma kuma daga gwamnatin Biden.

TikTok mallakin kamfanin ByteDance ne na kasar Sin, kuma dimbin 'yan siyasar Amurka sun zarge shi da kasancewa wata kafa ta aikin farfaganda da Beijing ke amfani da shi, lamarin da kamfanin ya musanta a lokuta da dama.

A cikin faifan bidiyon da shugaban ya wallafa a ranar Lahadi a kan kafar ta Tiktok mai dauke da asusun kamfen na @bidenhq, shugaban mai shekaru 81 ya tabo kan batutuwan da suka shafi siyasa har zuwa wasan zakarun NFL.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG