Dan takarar Democra Joe Biden yana zargin shugaban kasa cewa ya karaya a yaki da cutar coronavirus, yayinda shugaban kasa Donald Trump yake maidawa tsohon mataimakin shugaban kasar martani a wani gagarumin gangamin yakin neman zabe a jihar da ake kira fagen daga.
Donald Trump shine shugaban kasa mafi gazawa wurin aiki, mutumin da bai san aiki ba amma yake kokarin jan ragamar kasar cikin wannan annoba, inji Biden a lokacin da yaje jawabi ga tarin jama’a a Pennsylvania, a wani gangamin gaggawa da ya yi a kan hanyarsa da rana a jiyaLitinin.
Sa’o’I kalilin kafin haka, Trump ya kira abokin karawarsa a zaben ranar uku ga watan Nuwamba da dan takara mai ban tausayi kana ya musunta cewa gwamnatinsa ta karaya a yaki da coronavirus kamar yanda kempen Biden ke fadi.
Da yake jawabi ga manema labarai a filin saukar jirage na Allentown kafin taron gangaminsa na farko a cikin gangamin uku da ya yi a jiya Litnin a Pennsylvania da ake kwatantawa da filin daga, Trump yace Biden shine ya kara da rayuwa.
Amurka dai tana da mutane sama da miliyan takwas da dubu 600 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, adadin da ya haura kowace kasa a duniya kana mutum dubu 225 ne suka mutu da cutar.