Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN AMURKA:Tarihin Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyar Democrat Joe Biden


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Democrat Joe Biden
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Democrat Joe Biden

Abinda muka sani game da dan takakarar Shugaban kasa na Jam'iyar Democrat tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, dan jam’iyyar Democrats da ya shirya kalubalantar shugaba Donald Trump a zaben 3 ga watan Nuwamba, yana takarar shugaban kasa ne karo na 3, to amma wannan ne karo na farko da ya sami tikitin jam’iyyarsa na takarar shugaban kasa.

Idan ya yi nasar lashe zaben, aka kuma rantsar da shi a watan Janairu mai zuwa, Biden zai kasance shugaban Amurka na 46. A lokacin kuma zai kasance dan shekaru 78 da haihuwa, shugaban Amurka mafi tsufa a tarihi, inda zai zarta Trump mai shekaru 74.

A duk tsawon lokacin yakin neman zabensa Biden ya ce yana neman kawo karshen “dakunanniyar” gwamnatin Trump.

Biden ya fada a shafin yakin neman zabensa na yanar gizo cewa, “Muna fafutuka ne ta ceto Amurka”, “Lokaci yayi da za mu tuna ko mu waye. Mu Amurkawa ne: jajirtattu kuma tsayayyu, amma fa cike da buri a ko da yaushe. Lokaci yayi da za mu mutunta tare da girmama junanmu. Mu gina matsakaicin matakin al’umma da zai amfani kowa. Mu mai da martani akan mummunan amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da muke gani. Lokaci yayi da za mu kara matsa kaimi mu kuma tuna cewa akwai alherai da yawa a gaba.

Biden ya siffanta Trump a zaman shugaba maras alkibla da sam bai dace ba, yana mai cewa “Lokaci ya yi da za’a sami shugaba mai kima a duk fadin duniya, kuma shugabanci mai dattaku a cikin gida.

To amma a tsakiyar annobar coronavirus, yakin neman zaben Biden a farkon watan Yuli, ya sha bamban da yadda ake yakin neman zaben shugaban kasa a zamanin nan. Mafi akasari ya gudanar da yakin neman zabensa ne daga gidansa a gabashin jihar Delaware, tare da kai mamaya can ba’a rasa ba a Wilmington, birni mafi girma a jihar, da kuma jihohi na kusa kamar Philadelphia da Pennsylvania, domin gabatar da jawabai da tattaunawa da kananan tarukan jama’a.

Tsohon dan majalisar dattawan na Amurka ya gudanar da taron manema labarai sau daya tak a cikin tsawon watanni 3, kana kuma ya kauracewa manyan tarukan siyasa saboda fargabar kamuwa da cutar coronavirus ko kuma taimakawa yaduwar cutar idan mutane da yawa suka tattaru domin sauraren jawabinsa.

Joe Biden Dec. 12, 1972 lokacin da zaka zabe shi ya wakilci jihar Delaware a majalisar dattijai
Joe Biden Dec. 12, 1972 lokacin da zaka zabe shi ya wakilci jihar Delaware a majalisar dattijai

Bayan kammala karatun digiri a jami’ar Delaware, da kuma makarantar koyon aikin lauya ta Syracuse, Biden ya kasance dan majalisar dokoki mafi karancin shekaru da aka taba zabe a majalisar dattawan Amurka yana dan shekara 29, a shekarar 1972. Makwanni baya zabensa, wani mummunan al’amari ya faru.

Matar Biden da ‘yar su ‘yar shekara daya da haihuwa suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota yayin da suke sayayyar bikin kirsimeti. Biden ya yi tunanin yin murabus daga sabon mukaminsa na sanata domin kula da sauran ‘ya’yansu biyu duka maza, to amma kuma a maimakon haka, sai ya ci gaba da yin jeka-ka-dawo ta hanyar tafiyar jirgin kasa ta mintuna 90 a ko wace rana, tsakanin Washington da gidansa na Delaware, abinda ya ci gaba a dukkan wa’adi 6 da yayi na tsawon shekaru 31 a majalisar dattawa.

Shekaru bayan mutuwar matarsa, Biden ya hadu da Jill Jacobs Tracy, wata malamar makaranta, ya kuma aure ta, inda suka sami haihuwar ‘ya mace a shekarar 1981. Biden ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 1987 da 2007, to amma bai sami nasarar zaben fidda gwani ba. Bayan Biden ya fice daga takarar shugaban kasa a shekara ta 2007, dan takara a wannan lokacin Barack Obama, ya nemi yayi masa mataimaki. Suka lashe zaben shekara ta 2008, suka kuma yi ta zarce a shekara ta 2012. Biden yayi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa Obama na tsawon shekaru 8.

A haujin manufofin kasashen waje, yayin da yake a majalisar dattawa, Biden ya kasance dadadden memba a kakkarfan kwamitin hulda da kasashen waje, inda ya shugabanci kwamitin har sau 2. Ya kalu-balanci yakin gabar tekun Pasha a shekarar 1991, to amma kuma ya kada kuri’ar amincewa da mamayar kasar Iraqi a shekara ta 2003.

Ya yi fafutukar samun shigar Amurka da NATO a Bosnia a shekarar 1994. Yayin da yake a matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin Obama, Biden ya taimaka wajen shata manufofin Amurka akan Iraqi, ciki har da janye dakarun soji a shekara ta 2011. Haka kuma ya goyi bayan shigar rundunar sojin hadin gwiwa ta NATO a rikicin Libya a shekara ta 2011.

Biden ya kuma ba da gudummuwa sosai a lokacin da yake majalisar dattawa, musamman wajen shata kudurin dokokin yaki da miyagun laifuka, da suka hada da dokar haramcin mallakar miyagun makamai da ta yi aiki tsawon shekaru 10 har ya zuwa shekarar 2004 amma ba’a sabunta ta ba.

Ya goyi bayan hukunci mai tsanani ga wadanda aka sama da aikata manyan laifuka, matsayin da ya sabunta a yakin neman zabensa na shugaban kasa na shekarar 2020. A yanzu ya ce “an daure mutane da dama a kurkuku a Amurka – kuma da yawansu bakar fata ne.”

Joe Biden lokacin yana shugaban kwamitin majalisar dattijai Oct. 12, 1991
Joe Biden lokacin yana shugaban kwamitin majalisar dattijai Oct. 12, 1991

Biden ya ce yana duba yiwuwar kafa dokar yaki da cin zarafin mata, muhimmiyar doka daya da ya taimaka ta sami amincewar majalisar dokoki a lokacin da yake majalisar dattawa. To amma bayar da bahasinsa a zaman tantance nadin alkalin kotun koli Clarance Thomas, wani bakar fata mai ra’ayin rikau da shugaban kasa na lokacin George H.W. Bush ya gabatar, ya tunzura wasu ‘yan adawar Biden a cikin jam’iyyar Democrats tsawon shekaru.

Anita Hill, wata lauya, kuma abokiyar aikin Thomas, ta zargi Thomas da cin zarafinta amma Thomas ya musanta zargin. To sai dai Biden, a lokacin yana shugaban kwamitin majalisar dattawa na shari’a, bai ba da dama ga wadanda za su ba da shaida akan zargin na Hill ba.

Kungiyoyin mata da na masu fafutukar adalci a shari’a sun soki lamirin yadda Biden ya gudanar da zaman sauraren lamarin. Daga karshe kuma majalisar Dattawa ta amince da nadin Thomas a kotun koli har kawo yau. A watan Afrilun shekara ta 2019, Biden ya kira Hill domin nuna nadamarsa akan yadda ya gudanar da lamarin na Thomas, amma daga bisani ta ce sam ba ta gamsu ba.

Shugabancin Biden kan iya kasancewa irin shekaru 8 na wa’adin mulkin Obama, tare da manufofin da za su fadada tsare-tsaren ‘yan rajin samar da ci gaba akan daidaiton jinsi da ‘yancin mata a Amurka da ma sauran kasashen duniya. Yayin da Trump ya fitar da Amurka daga yarjeniyoyin cinikayya na kasa-da-kasa, da na nukiliya da sauyin yanayi da yake ganin ba sa cikin muradun Washington, ana sa ran Biden ya dawo da matsayin Amurka da shigarta al’amuran kasashen waje.

A cikin gida, Biden ya yi suna na tsawon shekaru, na bin hanyoyin siyasa domin yin aiki tare da ‘yan majalisar dokoki na Republican. To sai dai a tsawon lokacin da ya kwashe yana neman jam’iyyar Democrats ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, Biden ya maida martani akan sukar da ake masa, cewa bai da sassauci a jam’iyyar Democrats ta wannan zamani, yana mai fada a wani taro a watan Maris cewa “Na fi kowa ra’ayin ‘yan rajin ci gaba daga cikin masu takara.”

Biden ya jaddada nasarorin gwamnatin Obama, da suka hada da bunkasa sha’anin kiwon lafiya, goyon bayan fafutukar halatta auren jinsi, da fafutukar tallafin gwamnati domin ceto kamfunan kere-kere na Amurka.

Biden ya bayyana cewa Trump ya yi watsi da yaki da annobar coronavirus, ya kara da cewa zai “kai karshen saka siyasa da rashin fadar bayanai na gaskiya da suka kara uzzura rudani da nuna bambanci.” Biden ya ce zai “tabbatar da cewa kwararru a fannin kiwon lafiya ne za su shata manufofin gwamnati akan sha’anin na kiwon lafiya, ba ‘yan siyasa ba.”

Joe Biden da matarsa Jill
Joe Biden da matarsa Jill

A yayin da bayyana bacin rai da tunzurawa a shafin twitter ya zama babbar dabi’a ga shugaba Trump, subul-da-baka na kwabar da Biden ke furtawa, ya baiwa Trump damar ikirarin cewa dan takarar na Democrats yana samun disashewar kwakwalwa a yayin da yake kara tsufa. A ‘yan makwannin baya-bayan nan, Biden ya ce yana takarar majalisar dattawa, a maimakon shugaban kasa, haka kuma ya fada a wani lokaci cewa Amurkawa miliyan 120 suka mutu sakamakon cutar coronavirus, a maimakon dubu 120.

Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa “da ni ne na ke yin irin wannan kwabar, da kafafen yada labaran kanzon kurege sun yi caa a kai na. Wannan ya wuce kuskure na al’ada.”

To amma da aka tambaye shi ko kwakwalwarsa ta soma ja da baya, Biden ya ba da amsar cewa “Duba, abin da za ku yi kawai shi ne ku lura da ni, kuma ba zan jira ma a kwatanta kaifin hankali na da kaifin hankalin abokin takarar ta ba.”

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG