Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN AMURKA: Tarihin Dan Takarar Jam'iyar Republican Donald Trump


Trump and Biden face off in final presiden
Trump and Biden face off in final presiden

Donald J. Trump, shugaban kasar Amurka na 45, kuma shugaba na 3 da aka tsige shi amma kuma ya sami kubuta, yana neman sake zabensa a wa’adin mulki na 2 a watan Nuwamba.

A hukumance Trump ya kaddamar da yakin neman zabensa a watan Yunin shekara ta 2019 a Orlando ta jihar Florida, inda ya kaddamar da taken “ci gaba da bunkasa Amurka” (wato “Keep America Great” a turance), domin banbantawa da takensa na shekarar 2016, wato “Sake bunkasa Amurka” (Make America Great Again” a turance. Ya fadawa magoya bayansa cewa “mun taba yi a can baya, kuma za mu iya sake yi a yanzu, kuma wannan lokacin, za mu kammala aikin.”

Kafin ya zamo shugaban kasa, Trump hamshakin dan kasuwa ne da ke sha’anin gidaje a New York, kuma mai gabatarwa a tashar Talabijin. Bayan kammala karatun digiri a kwalejin nazarin sha’anin kudi ta jami’ar Pennsylvania, ya ci gaba da shugabancin sana’ar gidansu ta sha’anin gidaje da kadarori, inda ya fadada ta ya kuma giggina otal-otal, da gidajen caca da filayen wasan gulf a fadin duniya.

Donald Trump a Nov. 5, 1996, lokacin yana harkar gidaje
Donald Trump a Nov. 5, 1996, lokacin yana harkar gidaje

A farkon shekarun 1990, bisa tilas Trump ya gabatar da koken karyewar kasuwancinsa a Atlantic City da New York. To amma duk da haka ya sake ta da komadar kasuwancin nashi, inda a shekara ta 2016, Forbes ya kiyasta kadarorinsa a kan kudi dala biliyan 3 da miliyan 700. A shekara ta 2004, Trump ya kasance wani sanannen mutumin kafafen watsa labarai, saboda shiryawa da kuma fitowa a shirin nan na “The Apprentice”, wanda ya fice sosai a gidan talabijin na NBC. Ya bar shirin a shekara ta 2015, sa’adda yake shirin tsayawa takarar shugaban kasa.

A cikin shekaru 3 da rabi na mulkinsa, shugaba Trump ya zartar da wani babban kudurin dokar yin garambawul ga haraji, ya rage yawan sojojin Amurka a Syria, kana kuma ya sami nasarar amincewar majalisar dattawa akan alkalai 2 da ya nada a kotun koli, mai ra’ayin rikau Neil Gorsuch da Brett Kavanaugh, domin cike gibin da ke akwai a kotun mai alkalai 9. Haka kuma ya sami amincewar nada wasu alkalai kusan 200 na kananan kotunan tarayya. Nadin Kavanaugh musamman ya janyo cece-kuce, inda aka gudanar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a akan halayyarsa ta shan barasa yana matashi, da kuma zarge-zargen cin zarafin mata. Daga karshe dai, majalisar Dattawa ta amince da nadin na Kavanaugh a kotun kolin da rata kalilan.

Trump ya yi kokarin shata manufofi na dakile shigowar bakin haure, ciki har da samun nasarar amincewar majalisar dokoki, na kudi kusan dala biliyan 1 da miliyan 400, domin gina katangar kan iyaka (duk da yake yana kasa da adadin kudin da ya nema) ya kuma ayyana dokar ta baci domin samun karin dala biliyan 3 da miliyan 600 na ci gaba da aikin ginin.

Shugaban kasar ya cika alkawarin da yayi a lokacin yakin neman zabe, na janye dokokin gwamnati tare da soke kaso mafi yawa na shirin inshoran lafiya na tsohon shugaban kasa Barrack Obama da aka fi sani da Obamacare.

Duk da kasancewar miliyoyin Amurkawa sun rasa ayyukansu da inshorar kiwon lafiya sa’adda annobar coronavirus da ta addabi duniya ta yi lahani sosai a Amurka a wannan shekara, Trump ya nemi kotun koli da ta soke shirin na Obamacare baki dayansa. Trump ya yi ta bayyana rashin kaunarsa akan manufofin Obama, dan jam’iyyar Democrats da ya gada, wanda kuma shi ne kadai bakar fata da ya taba shugabantar kasar.

Shugaba Donald Trump yana nuna wani kudurin shugaban kasa da ya sa hannu
Shugaba Donald Trump yana nuna wani kudurin shugaban kasa da ya sa hannu

Trump ya samu bunkasar tattalin arziki na tsawon shekaru uku a karkashin mulkinsa, da ya hada da raguwar rashi aikin yi zuwa kashi 3.5 kacal a cikin dari, adadi mafi karanci da aka taba samu a kasar da ta fi karfin tattalin arziki a duniya a cikin shekaru 50, yayin da kuma Farashin hannayen jarin kasar suka daga sama. To sai dai kuma nasarar ta kai karshe ba shiri, a yayin da annobar coronavirus ta watsu daga China zuwa sassan duniya a farkon shekarar nan ta 2020, inda shugaba Trump ya yi ta bayyana shakku da tababa akan muni da kuma lahanin cutar ga Amurka.

A karshen watan Fabrairu, Trump ya yi hasashe a wani jawabin da yayi a gidan talabijin cewa “cutar zata gushe. Wata rana za ta gushe tamkar wata mu’ujiza.”

To sai dai a maimakon haka, cutar ta yadu zuwa dukkan jihohi 50, inda ta haifar da tsayawar al’amura cak. Nan take kuma kasar ta shiga cikin wani mawuyacin halin tattalin arziki. Fiye da ma’aikata miliyan 48 suka rasa aikinsu – adadin da ya kai fiye da rubu’in ma’aikatan Amurka – a yayin da gwamnonin jihohi suka ba da umarnin rurrufe kasuwanci, a kokarin hana yaduwar cutar. An rufe makarantu da jami’o’i, inda aka koma karatu daga gida. An dakatar da gasannin wasanni, yayin da asibitoci suka dakatar da wasu ayyukansu, su kuma shagunan sayar da abinci suka koma dauki-ka-tafi, yayin da aka haramta cin abinci a shagunan a mafi akasarin yankunan Amurka.

Trump ya gabatar da yi wa manema labarai bayani a kowace rana ta Allah akan cutar ta coronavirus na tsawon makwanni, to amma yayi ta bayyana saukin lahanin cutar, wata kila saboda fargabar bayyana ainihin garkiyar lamari akan cutar, kan iya haifar da cikas ga damarsa ta samun nasarar zaben watan Nuwamba.

Ya kafe da yin alkawarin cewa za’a samar da riga-kafin cutar nan da ‘yan watanni masu zuwa, duk kuwa da cewa kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce ba za’a iya kai ga samar da sahihin riga-kafi ba har sai ya zuwa farkon shekara ta 2021. Trump ya dauki lokaci yana koda maganin zazzabin maleriya wato Hydroxychloroquine a zaman maganin cutar ta coronavirus, yana mai cewa shi kan sa ya sha maganin. To sai dai kuma binciken da aka yi a kasashe da dama ya nuna cewa maganin baya da wani amfani wajen kula da masu cutar, don haka Trump ya daina ambatar maganin. A yayin da masana kiwon lafiya suka yi kira ga Amurkawa da su saka takunkumin rufe baki da hanci domin rage yawan yaduwar cutar, Trump ya yi kunnen kashi da kiran, yana mai cewa ba ya tsammanin don shi aka yi, kana kuma yana kushe masu saka takunkumin.

Sannu a hankali, makwanni bayan makwanni, adadin wadanda suka mutu ya zarta dubu 223 a Amurka ya zuwa 24 ga watan Oktoba, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai fiye da miliyan 8, adadin da ya fi na kowace kasa a duniya. Kwararru a fannn kiwon lafiya na hasashen cewa dubban wasu Amurkawa za su mutu a watanni masu zuwa.

A yayin da yawan kamuwa da cutar ya soma ragewa a jihohin da ke Arewacin Amurka, an sami sababbin barkewar cutar a jihohin kudanci, inda gwamnoninsu na daga cikin wadanda suka soma janye dokokin takaita zirga-zirga a al’ummominsu, daga nan kuma suka ba da umarnin sake rurrufe wuraren shan barasa da sauran sanao’i.

Shugaba Donald Trump yana kan hanyar asibiti bayan kamuwa da Coronavirus
Shugaba Donald Trump yana kan hanyar asibiti bayan kamuwa da Coronavirus

Adadin rashin aikin yi a Amurka ya kai har kashi 14.7 cikin dari, kana kuma ya sauka zuwa kashi 11.1 cikin dari a cikin watan Yuni, sa’adda aka sami karin ayyukan yi kusan miliyan 5. Trump wanda ya kasance ‘magori wasa kan-ka-da-kan-ka’, ya ce za’a kai ga kwanakin da al’amura za su daidaita ga tattalin arzikin Amurka a rabi na karshe na shekarar 2020, da kuma zuwa shigowar shekara ta 2021.

A yayin da cutar coronavirus ta ke ci gaba da karade Amurka, Trump ya fuskanci zanga-zanga, wadda a wasu wurare ta rikide zuwa tarzoma a fadin kasar, biyo bayan mutuwar wani bakar fata George Floyd a ranar 25 ga watan Mayu, wanda wani dan sanda farar fata ya danne masa wuya da gwiwar kafarsa, duk kuwa da cewa Floyd ya yi ta ihun cewa baya iya numfashi.

Trump ya aike da sakwanni iri daban-daban akan zanga-zangar da ta biyo baya, yana bayyana goyon bayan zanga-zangar lumana, amma kuma yana cewa rera taken “Rayuwar Bakar Fata Na Da Muhimmanci”, alama ce ta nuna kyama da kiyayya. Ya bayyana amincewarsa da wani hoton bidiyon daya daga cikin magoya bayansa da ya yi taken “karfin Farar Fata” to amma ya cire bidiyon daga shafinsa na twitter, bayan da masu suka suka ta sa shi gaba, a yayin da jami’an Trump suka ce ba su ji kalamin na wariyar launin fata ba.

A yayin da Amurka ke bikin cika shekaru 244 da samun ‘yancin kai a ranar 4 ga watan Yuli, Trump ya kara jaddada kalamansa, yana mai bayyana masu zanga-zangar neman adalcin launin fata a zaman “miyagun” wakilan wata sabuwar “fafutukar ‘yan kama karya masu tsattsauran ra’ayi”, wadanda manufarsu shi ne “wargaza Amurka.”

Sakamakon faruwar al’amura da dama a rabin farkon shekara ta 2020, babu tabbas akan makomar siyasar Trump, a yayin da kuri’un jin ra’ayoyin jama’a da dama suke nuna yana bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da kusan maki kashi 9 cikin dari, watanni 4 kafin zaben na shugaban kasa da ake gudanarwa bayan kowace shekara 4. To amma fa shugabannin Amurka biyu ne kacal suka taba shan kasa a kokarin neman wa’adin mulki na 2 a cikin shekaru 40 da suka gabata, haka kuma magoya bayan Trump na bayyana cewa ko a zaben shekara ta 2016, yana baya a kuri’un jin ra’ayoyin jama’a, sa’adda a ba zata ya kayar da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton.

A sha’anin lamurran kasashen waje, tsarin Trump ya yi suna akan manufarsa ta “Amurka ce Kan Gaba” wadda ya sa muradun Amurka sama da na kowa a duniya. Ya janye daga yarjeniyoyin kasa-da-kasa da dama, ciki har da yarjejeniyar kasuwanci ta yankin Pacific, yarjejeniyar kula da yanayi ta Paris da kuma yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran.

A bangaren kasuwanci kuma, Trump ya cika alkawarin da yayi a lokacin yakin neman zabe na dawo da yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shamaki ba ta nahiyar Amurka ta Arewa da kasashen Canada da Mexico, a yayin da kuma ya kaddamar da yakin kasuwanci da China. Ya yi ta nanata saka ayar tambaya akan yawan kudaden da Amurka ke kashewa wajen kariyar wasu kasashe, haka kuma ya fito karara ya soki lamirin kungiyar NATO, kungiyar hadakar dakarun soji da aka kafa ta bayan yakin duniya na 2.

Shugaban kasar yana da dangataka mai tsami da shugabannin kasashe da dama, ciki har da kawayen Amurka kamar tsohuwar shugabar Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron, to amma kuma ya rungumi dadaddun abokan hamayya irin shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un. Trump ya bayyana Kim a zaman “karamin dan sababi”, amma daga baya kuma ya sadu da shi har sau 3, inda ya tabbatar da cewa sun “kulla kyakkyawar dangantaka.”

Donald Trump a tron kasashen masu karfin masana'antu
Donald Trump a tron kasashen masu karfin masana'antu

A bangaren kalu-balen shugaban kasa kuma, ko baya ga annobar coronavirus da komadar tattalin arziki a shekara ta 2020, Trump ya fuskanci kalu bale da dama, da suka hada da zaman jin bahasin tsige shi da ‘yan Democrats suka shirya bisa zargin cewa Trump ya nemi Ukraine ta taimaka masa wajen bankado bayanai akan dan tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, wato Hunter Biden, da za su iya kawo cikas ga kudurin Biden na kokarin kalubalantarsa a zaben shekarar 2020.

Shugaba Donald Trump, da madakinsa Melania Trump da dansu, Barron Trump
Shugaba Donald Trump, da madakinsa Melania Trump da dansu, Barron Trump

Majalisar Wakilai mai rinjayen ‘yan Democrats ta tsige shi a karshen shekara ta 2019, to amma majalisar dattawa mai rinjayen ‘yan Republican ta wanke shi a farkon shekara ta 2020, inda dan majalisar dattawan na jam’iyyar Republican daya ne kacal ya jefa kuri’ar goyon bayan cire shi daga mulki. Haka kuma Trump ya fuskanci bincike na tsawon kusan shekaru 2, a karkashin jagorancin Robert Mueller, wanda ya gudanar da bincike akan ko Rasha ta yi katsalandan a zaben shekara ta 2016.

Rahoton karshe na Mueller ya gano cewa kwamitin yakin neman zaben Trump, bai hada kai da Rasha domin sauya sakamakon zaben ba. Ala ayyi halin, akwai wata dadaddiyar al’ada a Amurka, ta cewa ba’a tuhumar shugaban kasa da manyan laifuka, sa’adda ya ke kan mulki.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG