Bayern Na Tattaunawa Da Likitocin Hukumar Kwallon Kafar Senegal Kan Raunin Da Mane Ya Ji

Dan wasan Bayern Munich/ Senegal, Sadio Mane

Bayern ba ta yi karin haske kan girmar raunin na Mane ba, sai dai ta ce ba zai buga wasanta da Schalke a ranar Asabar ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke gasar Bundesliga a Jamus, ta ce tana tuntubar likitocin hukumar kwallon kafar Senegal saboda raunin da dan wasanta Sadio Mane ya ji.

Mane ya bugu a kafarsa ta dama a karawar da suka yi da Werder Bremen a ranar Talata, inda Bayern ta lallasa Bremen din da ci 6-1.

Wannan al’amari ya sa aka fara fargabar mai yiwuwa, Mane ba zai samu zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a wannan wata ba.

“Cikin kwanaki masu zuwa, za mu ci gaba da duba lafiyarsa. FC Bayern na kuma tuntubar likitocin hukumar kwallon kafar Senegal.” Wata sanarwa da Bayern ta fitar a ranar Laraba ta ce kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Bayern ba ta yi karin haske kan girmar raunin na Mane ba, sai dai ta ce ba zai buga wasanta da Schalke a ranar Asabar ba.

Senegal wacce ke rukunin A, za ta fara karawa da Netherland a wasanta na farko a gasar ta cin kofin duniya a ranar 21 ga watan Nuwamba.