Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mane Ya Ci Kwallonsa Ta Biyar A Bayern


Sadio Mane
Sadio Mane

A ranar Laraba Bayern ta lallasa Viktoria Cologne da ci 5-0, inda Mane ya ci kwallo ta uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a gasar German Cup.

Dan wasan Bayern Munich Sadio Mane na ci gaba da tabbatarwa da sabuwar kungiyarsa cewa ba ta yi zaben tumun dare ba, bayan da ya zura kwallonsa ta biyar a wasanni shida.

A ranar Laraba Bayern ta lallasa Viktoria Cologne da ci 5-0, inda Mane ya ci kwallo ta uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a gasar German Cup.

Yanzu Bayern ta kai zagaye na biyu kenan a gasar.

Mane, wanda dan salin kasar Senegal ne, ya koma Bayern daga kungiyar Liverpool da ta zo ta biyu a gasar Premier League a kakar wasan da ta wuce.

Wannan tawagar ‘yan wasa ta Bayern, ta sha banban da wacce ta kara da Borussia Moenchengladbach a karshen makon da ya gabata.

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar, Julian Nagelsmann, ya shigo da sabbin ‘yan wasa bakwai a wanna karawa da Cologne.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG