WASHINGTON, D. C. - Kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka na fuskantar matsalar rashin tsaro daga masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas, da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a arewa maso yammacin kasar da kuma wasu kungiyoyin masu aikata laifuka da ke yawo a kasar.
Jaridun kasar sun ruwaito a ranar Alhamis din da ta gabata cewa wasu da ake zargin mayakan wata kungiya mai da'awar kishin Islama ne suka kai hari a wani shingen binciken sojoji a wani yanki da ke kan iyakar Abuja da jihar Neja, inda suka kashe wasu sojoji.
Sojojin Najeriya da 'yan sandan kasar ba su amsa bukatar jin ta bakinsu kan harin da aka ruwaito ba.
Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) na kasa, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya kawar da fargabar mazauna yankin dangane da “barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan,” wanda bai yi cikakken bayani ba.
Adejobi ya ce NPF tana tura “karin jami’an ‘yan sanda da kadarorin aiki a cikin babban birnin tarayya da kewaye domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna ciki, muhimman kadarorin kasa da kuma wurare masu rauni.
Najeriya na da ‘yan sanda sama da 350,000, wanda masu sharhi kan harkokin tsaro ke ganin bai isa ba wajen samar da ingantaccen tsaro a kasar da ke da mutane sama da miliyan 200.
-REUTERS