Labarin daukar karin matakan tsaro a cikin Abuja da Kano na daga lamuran da ke kara nuna ba a samu bakin zaren warware kalubalen tsaron.
Duk da ya ke dama a duk shekarar zabe ko yakin neman zabe a kan iya samun irin wannan barazana da kan hana mutane sukuni.
Rashin tsaron ya sa mutane na zama cikin takatsantsan da kuma yin addu’ar neman kariya daga Allah.
Shugaban amintattu na gamaiyar kungiyoyin arewa Nastura Ashir Sharif ya ce gwamnatin na baiyana cewa ta na ware makudan kudi kan tsaro amma kamar ba a gani a kasa.
Fadar Aso Rock dai kan ce a rika fidda siyasa a lamuran tsaro don har indai za a cimma nasara kan samar da tsaro sai kowa ya ba da hadin kai.
Lokaci-lokaci za ka ga an raba lambobin gaggawa na tuntubar jami’an tsaro don bugawa da zarar an ga abin da ba a amince da shi ba.
Shin lambobin su na amfani ko kuwa a’a, ingantar tsaron zai zama amsa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: