A ranar da aka ware domin hankalin jama'a kan illolin shan tabar sigari ta wannan shekarar, Hukumar Lafiya ta Duniya ta hada hannu da Hadakar kungiyoyin yaki da cututtuka masu adabar zuciya ko WHF domin wayar da kan jama'a game da yadda shan taba ke haddasa cututtukan zuciya da ke hallaka kimanin mutane miliyan 17.9 a duk shekara.
Shan taba da kuma shakar hayakin tabar ga wadanda ba su sha, sune ke kan gaba wajen haddasa cututtukan zuciya da suka hada da bugun zuciya wato zuciya ta daina bugawa, da shanyewar bangaren jiki wato stroke, wadanda ke hallaka kimanin mutane miliyan 3 duk shekara.
"Yawanci ana sane da cewa shan taba na haddasa cutar sankara ko cancer a turance amma da dama ba su san cewa ta na haddasa ciwon bugun zuciya da shanyewar bangaren jiki ko stroke ba," inji Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban sashen yaki da cututtukan zuciya na hukumar lafiya, Dakta Douglas Bettcher, ya ce gwamnatocin kasashe na da karfin ikon kare jama'arsu daga kamuwa da wadannan cuttukan.
"Ta hanyar samar da matakan da za su taimaka wajen rage barazanar cututtukan zuciya kamar haramta shan taba a duk wuraren da ba a waje ba ne ba da kuma saka gargadi kan kwalayen tabar sigari da ke nuni da hadurran da ke tattare da shan tabar," inji Dakta Bettcher
A kowace shekara, shan tabar sigari na hallaka sama da mutane miliyan 7 duk da cewa ana samun raguwar shan tabar kamar yadda sabon rohoton hukumar lafiya 'Global Report on Trends in Prevalence of Tobacco Smoking 2000-2025' ya nuna.
Rohoton ya nuna cewa an samu raguwa, inda a shekarar 2000 kashi 27 cikin dari na jama'ar duniya ne ke shan taba amma a 2016, kashi 20 cikin 100 aka samu.