Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Rage Shekarun Tsayawa Takara


Shugaba Buhari bayan ya rattaba hannu kan dokar 'Not Too Young To Run'
Shugaba Buhari bayan ya rattaba hannu kan dokar 'Not Too Young To Run'

Shugaba Buhari ya cika alkawalin da ya yi a ranar Dimokradiyya game da rattaba hannu kan dokar rage shekarun tsayawa takarar shugabanci a Najeriya.

Shugaban ya rattaba hannun yau Alhamis kan kudirin rage shekarun tsayawa takara na 'Not Too Young To Run' a zauren majalisar zartaswarsa na fadar shugaban Najeriya a Abuja.

Dokar za ta rage shekarun tsayawa takarar shugaban kasa daga 40 zuwa 30; gwamna daga 35 zuwa 30; 'yan majalisar dattawa daga 35 zuwa 30; majalisar wakilai kuma daga 30 zuwa 25.

Yanzu haka dai matasan na bayyana farin ciki dangane da wannan alkawari na Shugaba Buhari na saka hannu akan wannan doka.

"Wannan alkawali da ya yi na sa wa wannan doka hannu da muka dade muna rajin ganin cewa ta tabbata ta zama doka kuma muna godiya," inji Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata, na daga cikin matasan da suka yi gangami a kwanakin baya domin matsa lambar ganin Shugaba Buhari ya saka hannu akan wannan doka.

A cewarsa, matasa sun yi nisa ta bada gudunmuwarsu ta bangarori da dama wajen ci gaban al'umma kuma wannan dokar za ta basu wata dama da za su kara zage damtse wajen taimakon kasa.

Sai dai masana harkokin siyasa na ganin cewa da wuya dokar rage shekarun tsayawa takarar zaben ta yi tasirin da ake bukata.

Malami a Jami’ar Bayero Kano, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bayyani kan tasirin dokar inda ya ce ya karkasu gida biyu.

"Akwai tasiri na ji, akwai na gani. Wato yanzu dokar za ta samu tasirin ji, ma'ana za su ji dadi cewa an kulasu, an kuma yarda da abun da suke so. Amma akwai tasiri na gani, wato su iya aiwatar da wani abu har su sami nasarar da suke bukata. Wato su iya fitowa takara su kuma ci. Wannan wani abu ne zaman kansa wanda a karnin da muke ci ki yanzu, zai yi wahala." inji Dakta Dukawa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG